Connect with us

Labarai

‘Yan bijilante sun kama matasan da ke addabar unguwa da sata

Published

on

Kungiyar sintiri ta Bijilante da ke unguwar Gaida a karamar hukumar Kumbotso ta kama wasu matasa biyu da a ke zargin sufasa kantinan a yankin.

Daya daga cikin ‘yan kwamitin unguwar, Alhaji Abdullahi Yarima a zantawar sa da gidan rediyon Dala a ranar Litinin ya ce, “A lokacin Corona a jikin gidana akwai wani bawan Allah da su ka shiga kantin sa su ka yashe masa kaya, shekara goma kullum za mu fito muna zagaye, amma da mun koma gida sai mu ji cewar an yi sata, wanda ya nuna barawon ya na kusa damu”. Inji Alhaji Abdullahi

Suma matasan da a ke zargin sun bayyana cewar, “Sunana Ammar Yasir, mun dauki inji a shago, sai dai Allah ya kara kiyayewa. Sunana Anas Ahmad, shagunan mutane muka bude guda biyar, muka debi kaya, ina da sana’a ta Plamba, mun je wani kanti da shagon atamfofi, abu ne ya faru amma in Allah ya yarda ba za mu sake yi ba”.

Haka zalika, Kwamandan Bijilante na yankin Aliyu Sharif Jikan Nana ya ce, “Yaran sun addabi unguwa, mu da kan mu mu na kwaye, amma mun kasa kama su, yanzu ga shi sun zo hannu, za mu tabbatar an hukunta su domin ya zama darasi ga wasu a unguwar”.

Wakiln mu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewar, Alhaji Abdullahi Yarima ya kuma yi kira ga iyaye da su rinka sa’ido a kan ‘ya’yan su domin an sha kai korafin daya daga cikin su a na zargin sa da sata a unuguwar amma mahaifiyar sa ta na cewa ba shi ba ne.

 

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Labarai

Dilolin Wiwi sun yanki mai unguwa da Wuƙa, tare da cizon shi a hannu, kan ya shana su sha da siyar da wiwi a Kano

Published

on

Wasu matasa da ake zargin ƴan Daba ne, kuma dilolin Wiwi, sun kai wa mai unguwar yankin Bachirawar Tukwane ƙarshen kwalta hari da muggan makamai.

Tun farko dai mai unguwar yankin Malam Mustapha ya shawarci matasan ne, da su dai na ɗaurin tabar Wiwi, da siyar wa a kofar gidajen mutane lamarin da ya tunzura matasan.

Matasan dai sun rutsa mai unguwar Bachirawar ne inda suka yi yunƙurin hallaka shi, bayan da suka yanke shi da Wuƙa, tare da cizon sa a Hannu, sai dai ‘yan ƙungiyar bijilante na yankin sun kawo masa ɗauki inda suka kama wani matashi mai laƙabin Kokuwa.

A lokacin ne kuma mutanen yankin suka yi yunƙurin ɗaukar doka a hannu, sai dai mai unguwar Bachirawa Malam Mustapha dan Bachirawa Gabas Malam Abdulkadir Dandiyo, sun kuɓutar da matashin inda aka mika shi ofishin ƴan sanda, ragowar matasan suka tsere.

Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar yankin Dakta Jibrin Sagir, ya ce a shirye suke su tinkari duk wani ɓata gari a yankin da yake addabar su.

Continue Reading

Trending