Connect with us

Labarai

An kubutar da wani mutum da a ka sakawa sasari tsawon shekaru 30

Published

on

Kungiyar kare hakkin dan adam mai suna Human Right Network, ta kubutar da wani mutum mai suna Murtala Muhammad mai shekaru 55, daga daurin Sasari da a ka yi masa a gida tsawon shekaru 30, a Kofar Fada da ke karamar hukumar Rogo a jihar Kano.

Shugaban kungiyar, Kwamared AA Haruna Ayagi ne ya bayyanawa Dala FM hakan jim kadan bayan kubutar da Murtala daga tsare shin da a ka yi, saboda lalurar tabin hankali da ya ke fama da ita.

Ya ce, “A safiyar nan ne labari ya zo mana abun da mu ka dade mu na bincikawa, domin mu gano gaskiyar lamarin, an kulle shi a gidan ne tun shekaru talatin da su ka gabata lokacin ya na da shekaru ashirin da biyar da haihuwa”.

Ya kuma ce, “Iyayen sa sun daure shi ne ta hanyar saka masa sasari a kafa ,sakamakon lalurar kwakwalwa, kuma tuni mu ka sanar da ‘yan sandan yankin karamar hukumar Rogo da taimakon su  a ka garzaya gidan a ka kubutar da shi daga cikin kangin”. A cewar Kwamared AA Haruna Ayagi

Shi ma mutumin Murtala Muhammad wanda ya magantu da kyar ya ce, “Na ji dadi da a ka kubutar da ni, domin ba na samun abinci yadda ya kamata ga kuma rashin fita da ba na yi”. Inji Murtala.

Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito cewa, Kwamared AA Haruna Ayagi ya kuma ja hankalin iyayen da ke daure ‘ya’yan su da su guji yin hakan domin kungiyar su ba za ta bari a rinka cutar da su ba saboda matsalar tabin hankali.

Labarai

Zaman lafiya: Majalisar dinkin duniya ta taka rawa – Farfesa Kamilu Fagge

Published

on

Masanin kimiyar siyasa a jami’ar Bayero da ke jihar Kano Farfesa Kamilu Sani Fagge, ya ce majalisar dinkin duniya, ta taka rawa wajen samar da zaman lafiya a duniya.

Farfesa Kamilu Sani Fagge ya bayyana hakan yayin zantawa da wakiliyar mu Aisha Aminu Kundila a wani bangare na bikin ranar tunawa da majalisar dinkin duniya a wannan shekarar.

Ya ce, “Nijeriya ta zama mamba ce a majalisar ta dinkin duniya a 1960 a matsayin mamba ta 99”. Inji Farfesa Kamilu Sani Fagge.

Continue Reading

Labarai

Polio: Za mu dakile bullar cutar shan inna a Kano – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta ci gaba da sanya idanu, domin ganin ba a sake samun bullar cutar shan inna ba ta Polio a fadin jihar Kano.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan a yayin zantawar sa da manema labarai a wani bangaren na bikin ranar yaki da cutar shan inna ta duniya da ake gudanarwa a yau.

Ya ce, “Za mu ci gaba da gudanar da rigakafin cutar Polio a fadin jihar Kano, duk da cewa babu cutar a jihar wanda hakan zai bai wa yara kariya daga kamuwa da cutar a nan gaba”. A cewar Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa.

Sai dai ya bukaci iyaye da su ci gaba da kai yaran su, domin karbar rigakafin wanda hakan ne kadai zai taimaka wajen yaki da cutar ko da a nan gaba.

 

Continue Reading

Labarai

‘Yan sandan SARS 16 za su fuskanci hukunci sakamon zargin kisan kai

Published

on

Kwamitin shugaban kasa da ke bincike kan ayyukan ‘yan sanda ya ba da shawarar hukunta ‘yan sandan SARS 16 sakamakon zarginsu da kisan kai a jihohin kasar nan 12 har da birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun ce tun a watan Yunin shekarar da ta gabata ne kwamitin ya yi bincike kan mutanen, inda sai akwanan ne ya mikawa shugaban kasa rahoton.

Sauran wadanda aka mikawa rahoton sun hada da sufeto Janar na ‘yan sandan Muhammed Adamu da hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kasa da kuma attorney Janar na tarayya.

Jihohin da ‘yan sandan na SARS suka gudanar da ta’asar sun hada da: Akwa Ibom, Benue, Delta, Enugu, Lagos da Ogun, Rivers, Gombe, Kaduna da Kogi da kuma Kwara.

 

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!