Connect with us

Addini

Ba za mu lamunci wuce gona da iri a wakar yabo – Afakallah

Published

on

Hukumar tace fina finai ta jihar Kano ta ce, ba zata lamunci yadda masu yabon fiyayyan halitta annabi Muhammad S A W su ke wuce gona da iri ba musamman a cikin wakokin su na yabo.

Shugaban Hukumar ta Kano Isma’il Na Abba Afakallah ne ya bayyana haka lokacin taron da Madrasatu Ahlu Faidatul Tijjaniyya ta shirya domin nuna rashin goyan bayan su kan masu yabon da ke wuce gona da iri da kuma yin addu’oi kan matsalolin tsaro da su ka addabi kasar nan.

Ya ce, “Lokaci ya wuce da masu yabon ma’aiki za su rika sakin baki kan janibin fiyayyen halitta Annabi S A W domin kuwa hukumar tace fina finai za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen kawo karshen matsalar domin ya sabawa addini”.

Ya kuma ce, “Kamata ya yi mutane su sani cewa, yabon Annabi ibada ce kuma addini ne saboda haka dole ne Hukumar ta rika daukar kwararan matakai a kan duk wanda ya ke neman wuce gona da iri a cikin yabon Annabi S A W ta hanyar tace duk wasu wakokin yabo”. A cewar Afakallah

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya rawaito cewa, shugaban Hukumar Afakallah ya kuma yabawa wadanda su ka kirkiro wannan makaranta domin za ta taimaka wajen kawo karshen baragurbin masu yabon Annabi a Kano domin ya sabawa koyarwar addini.

Addini

Matsin Rayuwa: Shugabanni ku sassautawa al’umma – Babban Limamin Kano

Published

on

Babban limamin Kano, kuma wanda ya jagoranci sallar idi a babban masallacin idin na Kofar Mata a nan Kano, Farfesa Muhammed Sani Zaharaddin, ya ja hankalin shugabanni da su sassautawa al’umma, sakamakon halin matsin rayuwar da ake ciki a yanzu.

Farfesa Muhammed Sani Zaharaddin, yayi jan hankalin ne yayin huɗubar da ya gabatar, bayan kammala sallar idi da ta gudana a yau Laraba, a babban masallacin idin dake unguwar Kofar Mata a Kano.

Ya kara da cewa kasancewar al’umma na cikin mawuyacin hali da kuncin rayuwa, akwai buƙatar shugabanni su yi bakin ƙoƙarin su, domin kawo sauki daga halin matsin halin rayuwar da ake fama dashi.

Yayin sallar Idin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da mataimakin sa Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da sauran al’umma da dama ne suka halarta.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Abba Haruna Idris ya rawaito cewa, Farfesa Muhammed Sani ya kuma ja hankalin al’umma, da su koma ga Allah Subhanahu wata’ala domin samun dacewa a Duniya da gobe Ƙiyama.

Continue Reading

Addini

Ku fara duban watan Sallah daga gobe Litinin – Fadar Sarkin Musulmi

Published

on

Yanzu haka kwamitin ganin wata na Fadar mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya buƙaci al’ummar musulmin ƙasar nan da su fara duban jinjirin watan Shawwal, daga gobe Litinin, 8 ga watan Afrilun, 2024 da ake ciki.

Bayanin hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar a yammacin yau Lahadi a jihar Sokoto.

Sanarwar ta ce, duk wanda ya ga watan Shawwal, ya sanarwa Mai Gari ko Hakimi mafi kusa wanda kuma zai sanar har zuwa fadar Sarkin Musulmi.

Har ila yau, fadar Sarkin musulmin ta kuma bayar da lambobin waya waɗanda mutane za su yi amfani da su wajen ba da rahoton ganin watan Sallah ga fadar Sarkin musulmin, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta BBC ta rawaito.

Continue Reading

Addini

Iyaye ku kula da tarbiyyar ƴaƴan ku – Malama Fatima Tsakuwa

Published

on

Malamar addinin musulunci dake nan Kano Malama Fatima Ahmad Tsakuwa, ta shawarci mata da su ƙara himma wajen kula da tarbiyyar ƴaƴansu, tare da kuma zaburar da su mahimmancin yin addu’a a cikin wannan wata na Ramadana, domin rabauta da rahamar Ubangiji S.W.T.

Malama Fatima Ahmad Tsakuwa, ta bayyana hakan ne yayin taron bita ta musamman da gidauniyar Bango Charity Foundation ƙarƙashin Malama Fatima Yusif Mai tama, wanda gidauniyar ta shirya wa Mata, da bitar ta shafi watan Azumin Ramadana, akan yadda iyaye matan za su kula da ƴaƴan su, da ya gudana a ofishin ƙungiyar dake unguwar Sharaɗa a Kano.

Wakiliyar tashar Dala FM Kano, ta rawaito cewa malama Fatima Tsakuwa ta ce akwai buƙatar iyayen su ƙara lura da tarbiyyar ƴaƴansu, tare da yawaita karatun Al-kur’ani mai girma domin rabauta da falala a wajen Allah S.W.T.

Continue Reading

Trending