Connect with us

Labarai

Rushewar gini ya jikkata mutane 3 da rasa rai a Kano

Published

on

Wani gida da ya rushe a unguwar ƙofar Kansakali layin Alhawali da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano, ya jikkata mutane uku tare da rasa ran yaro ɗaya.

Al’amarin ya faru ne da Asubahin yau Talata sakamakon ruwan sama da iska da a ka tafka, inda gidan wani Magidanci mai suna Alhaji Umar Baba ya ruso a kan ƴaƴansa, kuma a lokacin da magidancin ya je domin ganin abin da ya faru sai ginin ya ƙara ruftawa da shi.

Mai ɗakin magidancin Aisha Umar ta shaidawa Dala FM cewa, mai gidan ta da ƴaƴanta biyu suna asibiti a na ci gaba da duba lafiyar su, bayan da maƙota su ka kawo musu ɗauki, sai dai ɗanta guda ɗaya Muhammad Umar ɗan shekara 12 ya rasa ransa.

Wani daga cikin maƙota da suka kai musu ɗauki mai suna Muhammad Ibrahim ya ce, “Na fito zuwa masallaci kawai sai na ji ƙarar faɗuwar ginin wanda hakan ya sanya na gayyato al’umma muka kawo musu ɗauki”. A cewar Muhammad Ibrahim

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar al’amarin kamar yadda kakakinta Sa’idu Muhammad Sule ya tabbatar, ya kuma nemi al’umma da su riƙa ɗaukar mataki a duk lokacin da su ka lura da gini ya fara nuna alamun zaftarewa.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending