Connect with us

Labarai

Rikicin Siyasa: Ƴan sanda sun yi wa shalkwatar APC ƙawanya

Published

on

Jami’an tsaro a jihar Jigawa sun kewaye sakatariyar jam’iyyar APC mai mulki a jihar.

Rahotonni sun ce, an wayi gari da ganin jami’an tsaro a kan hanyoyin zuwa sakatariyar jam’iyyar da ke birnin Dutse.

Wakilin mu na jihar Jigawa ta tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ƴan sanda ta jihar Jigawa SP. Abdu Jinjiri.

Ya ce, “Mun girke ƴan sandan ne saboda wasu bayanan sirri da mu ka samu na yiwuwar afkuwar wani lamari a sakatariyar”. Inji SP. Abdu Jinjiri.

A ranar Litinin da ta gabata ne, gwamnan jihar Alhaji Badaru Abubakar ya jagoranci zama da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar ta APC a fadar gwamnatin Kano, wanda a yayin taron a ka sanar da dakatar da shugaban jam’iyya na jihar Alhaji Habibu Sani Sara.

Sai dai kwanaki biyu da wannan taro Alhaji Habibu Sara ya sanar da manema labarai cewa har yanzu shi ne shugaban jam’iyyar APC a jihar.

Habibu Sara ya yi zargin cewa, an bijiro masa da wannan batu ne saboda tarayyar sa da wasu mutane da gwamnatin jihar ba ta jituwa da su.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Rahoto: Saurayi ya kai iyayen budurwar sa kotu kan zargin cinye masa kudade

Published

on

Wani matashi ya yi zargin iyayen budurwar sa sun karbi kudaden aure har da sadaki a hannun sa, bayan ya rage kwanaki uku a daura aure, iyayen budurwar su ka kawar da maganar auren kuma tsawon watanni ba zancen aure ko kuma dawo masa da kudaden da ya bayar.

Sai dai iyayen budurwar sun yi da’awar cewar, an je gwaji ne kafin aure saurayin ya gudu, inda shi kuma ya mayar da martanin cewar, a ranar da a ka je gwajin bai je da isassun kudi ba, shi yasa ya tafi, kuma washe gari ko da yaje gidan budurwar bijiro da zancen ta fasa auren, yanzu tsohon saurayin ta za ta aura, hakan ta sanya ya garzaya kotun shari’ar musulunci domin a bi masa hakkin sa.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mai sayen filaye ya kai karar abokin cinikin sa kotu bayan shekaru 3

Published

on

Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a unguwar Goran dutse, karkashin mai shari’a Isma’il Garba Kofar Na’isa, wani mutum mai suna Ibrahim Ishaq, ya yi karar wani mai suna Ibrahim Abba, kan cinikin wani filaye da su ka yi shekaru uku da su ka gabata.

Ibrahim Abba ya bai wa Ibrahim Ishaq motoci guda biyu shi kuma ya bashi filaye guda tara, daga bisani takaddama ta barke a tsakanin su, Ibrahiim Ishaq ya na zargin an cuce shi a cinikin, hakan ya sanya shi garzaya wa kotu.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: NAFDAC ta kama magungunan dabbobi na jabu a Kano

Published

on

Hukumar lura da ingancin abincin da magunguna ta kasa reshen jihar Kano NAFDAC, ta kai sumame wani gida a karamar hukumar Bichi, ta ka kama  wani mutum Muhammad Jamilu Sani, wanda aka samu yana hada magungunan dabbobi da allurai da ta ke zargin na jabu ne.

Shugaban hukumar Malam Shaba Muhammad ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!