Connect with us

Lafiya

Har yanzu ‘yan Afrika ba su ci moriyar dimukradiya ba – Farfesa Kamilu

Published

on

Masanin kimiyyar siyasa da ke Jami’ar Bayero a jihar Kano Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce, mulkin dimukaradiyya a yankin Afrika bai yi tasirin da za a iya cewa, an ci moriyar sa ba yadda ya kamata, idan a ka yi la’akari da kasashen da suka cigaba.

Farfesa Kamilu Fagge ya bayyana hakan yayin zantawa da wakiliyar mu Maryam Ali Abdullahi a wani bangare na bikin ranar dimukaradiyya da a ke gudanarawa a ranar Talata.

Ya ce, “Mulkin Dimukaradiyya da wani tsari ne da zai bai wa al’umma da a ke mulka damar fadin albarkacin bakin su tare da zabar wadanda su ke da ra’ayi”. Inji Farfesa Kamilu Fagge

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Mun rufe wasu cibiyoyin lafiya a Kano don kazanta – Dr. Usman

Published

on

Hukumar kula cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu ta Jihar Kano, ta rufe wasu wuraren kula da lafiyar al’umma sakamakon rashin kwararrun ma’aikata da kuma gudanar da ayyukan su a harabar da ke cike da kazanta.

Babban sakataren hukumar Dr. Usman Tijjani Aliyu ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai a ranar Talata.

Dr. Usman ya kuma ce, hukumar za ta gurfanar da wadanda ta kama gaban kotu domin ta ci su tara a kan rashin samun lasisi kafin bude wuraren na su.

 

Continue Reading

Labarai

Za mu magance ƙarancin Unguzoma a asibitoci – Gwamna Badaru

Published

on

Ma’aikatar Lafiyar jihar Jigawa ta ce, za ta samar da mata masu karbar haihuwa domin magance matsalar karancin su a asibitoci musamman a lunguna.

Babban sakataran ma’aikatar lafiya na jihar Jigawa Dr. Salisu Mu’azu ne ya bayyana haka, yayin da yake ganawa da wakili Dala FM, a jihar Jigawa.

Ya ce, “Babbar matsalar da tafi damun ma’aikatar yanzu haka shi ne dabi’ar da wasu ma’aikatan lafiya ke da ita ta kin zuwa wurin da a ka turasu aiki musamman mata”.

Ya kuma ce, “Irin wannan dabi’a ce ta ke taimakawa wajen kawo cunkoson marasa lafiya a asibitocin birane, duk kuwa da kokarin da gwamnati ke yi na samar da makarantun koyar da aikin lafiya a jihar”. Inji Dakta Salisu Mu’azu

Dr. Salisu ya kuma kara da cewa, akwai takaici matuka kan wannan dabi’a, duba da yadda gwamnatin jihar Jigawa ta samar da asibitoci a kowacce mazaba amma irin wannan halayya na neman kawo nakasu kan wannan yunkuri.

Continue Reading

Labarai

Likitoci masu neman kwarewa sun shiga yajin aiki

Published

on

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a sakamakon rashin biyan mambobinta wasu hakkkokin su tun daga shekarar 2016 zuwa bana.

Shugaban kungiyar reshen Jihar Kano Dakta Abubakar Nagoma Usman ne ya bayyana haka a yayin taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a ranar Litinin domin shaidawa al’umma halin da a ke ciki game da yajin aikin.

Ya ce, “Akwai kudaden albashi da na alawus-alawus da kungiyar ke bin gwamnati, wanda har yanzu ba mu san matsayin mu a kan lamarin ba”.

Ya kuma ce, “Gwamnatin tarayya na korar mambobin mu daga aiki, duk da cewa sun sadaukar da rayuwarsu tun bayan barkewar annobar cutar Covid-19”. Inji Dakta Abubakar Nagoma Usman

Wakilinmu Bilal Nasidi Mu’azu ya rawaito cewa kungiyar ta ware wasu wurare domin duba marasa lafiya da ke bukatar kulawar gaggawa.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!