Connect with us

Labarai

Babu wanda ya cancanci shan romon dumukradiya sai talaka – Farfesa Kamilu Fagge

Published

on

Masanin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero da ke jihar Kano Farfesa Kamilu Sani Fagge, ya ce, babu wanda ya cancanci ya sha romon dumukradiya kamar talaka, duba da su ke jefawa shugabanni kuri’a har su samu su dare kujerar mulki.

Farfesa Kamilu Sani Fagge, ya bayyana hakan ne a zantawar sa da gidan rediyon Dala a ranar Alhamis

Haka zalika, shima wani masanin tattalin arziki a Jami’ar Yusuf Maitama sule da ke jihar Kano Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata ya ce, “Idan har gwamnatin kasar nan na san shawo kan matsalar halin matsin rayuwa da a ke ciki, babu shakka sai ta tuntubi shawararin masana kan harkokin tattalin arzikin”. Inji Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata

Wakiliyar mu Shamsiyya Farouk Bello ta rawaito cewa, a yayin da Najeriya za ta cika shekarun 60 da samun ‘yan cin kai a tafarkin dumukradiya, amma masana na ganin har dan Najeriya bai ci ribar dumukradiyar ba.

 

Labarai

Zaman lafiya: Majalisar dinkin duniya ta taka rawa – Farfesa Kamilu Fagge

Published

on

Masanin kimiyar siyasa a jami’ar Bayero da ke jihar Kano Farfesa Kamilu Sani Fagge, ya ce majalisar dinkin duniya, ta taka rawa wajen samar da zaman lafiya a duniya.

Farfesa Kamilu Sani Fagge ya bayyana hakan yayin zantawa da wakiliyar mu Aisha Aminu Kundila a wani bangare na bikin ranar tunawa da majalisar dinkin duniya a wannan shekarar.

Ya ce, “Nijeriya ta zama mamba ce a majalisar ta dinkin duniya a 1960 a matsayin mamba ta 99”. Inji Farfesa Kamilu Sani Fagge.

Continue Reading

Labarai

Polio: Za mu dakile bullar cutar shan inna a Kano – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta ci gaba da sanya idanu, domin ganin ba a sake samun bullar cutar shan inna ba ta Polio a fadin jihar Kano.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan a yayin zantawar sa da manema labarai a wani bangaren na bikin ranar yaki da cutar shan inna ta duniya da ake gudanarwa a yau.

Ya ce, “Za mu ci gaba da gudanar da rigakafin cutar Polio a fadin jihar Kano, duk da cewa babu cutar a jihar wanda hakan zai bai wa yara kariya daga kamuwa da cutar a nan gaba”. A cewar Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa.

Sai dai ya bukaci iyaye da su ci gaba da kai yaran su, domin karbar rigakafin wanda hakan ne kadai zai taimaka wajen yaki da cutar ko da a nan gaba.

 

Continue Reading

Labarai

‘Yan sandan SARS 16 za su fuskanci hukunci sakamon zargin kisan kai

Published

on

Kwamitin shugaban kasa da ke bincike kan ayyukan ‘yan sanda ya ba da shawarar hukunta ‘yan sandan SARS 16 sakamakon zarginsu da kisan kai a jihohin kasar nan 12 har da birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun ce tun a watan Yunin shekarar da ta gabata ne kwamitin ya yi bincike kan mutanen, inda sai akwanan ne ya mikawa shugaban kasa rahoton.

Sauran wadanda aka mikawa rahoton sun hada da sufeto Janar na ‘yan sandan Muhammed Adamu da hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kasa da kuma attorney Janar na tarayya.

Jihohin da ‘yan sandan na SARS suka gudanar da ta’asar sun hada da: Akwa Ibom, Benue, Delta, Enugu, Lagos da Ogun, Rivers, Gombe, Kaduna da Kogi da kuma Kwara.

 

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!