Connect with us

Labarai

Gidan ajiya da gyaran hali: Kansila ya samu gurbi a gidan saboda cin zarafi

Published

on

Kotun majistret mai zamanta a Airport karkashin mai shari’a Hajiya Talatu Makama ta aike da kansilan mazabar Bachirawa gidan kaso.

‘Yansanda ne dai suka gurfanar da kansilan Hon. Saddik Rabiu Zubairu, a kan zargin kansilan da lefin kutse da sanadin rauni da kuma keta alfarmar dan adam.

kunshin zargin ya bayyana cewar, kansilan Bachirawa Saddiku Rabiu ya balle kofar shagon wani matashi mai suna Auwalu mai Wake ya yi masa dukan kawo wuka daga karshe kuma su ka hadu shi da wasu karti sun ja Auwalun a kasa sun sanya shi a but din mota sun kai shi ofishin Anti daba saboda mai waken yace wa kansila ya ci taliyar karshe.

Tun a ranar Juma’ar da ta gabata ‘yansanda su ka gurfanar da su a gaban kotu amma da yake kotu wuri ne na adalci nan take mai shari’a Hajiya Talatu Makama ta bayar da belin kansila a ranar Juma’ar a ka kuma sanya yau Litinin domin a dawo kotu a ci gaba da shari’a.

Sai dai kansila bai samu damar halartar kotun ba sai bayan karfe 11 lokacin kuwa har an kirawo shari’ar sai dai a lokacin kansila bai karaso kotun ba.

Mai gabatar da kara ta roki kotun da ta karya belin tunda dai kotu ba ta jiran kowa sai dai a jira kotu kuma nan take kotun ta janye belin.

Yayin da kansilan ya bayyana a kotun ya nemi a yi masa hanzari kasancewar an wayi gari lauyansa baya jin dadi kuma shi ne ya kai lauyan asibiti sai dai kotun tayi watsi da rokon.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewar, Mai kara Auwalu mai Wake ya bayyanawa kotun cewar, bayan kansila akwai wani dogarin kansilan mai suna Ado Babba da kuma kanin kansila Hassan Rabi’u wadanda suka yi masa wannan cin mutunci amma kuma kansilan kawai aka gurfanar, koda yake ‘Yansanda masu bincike kuma sune suka tsame wadancan mutane 2 ita kuma kotu abin da yake gaban ta shi take saurara.

 

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending