Connect with us

Labarai

Al’umma su yiwa Nijeriya addu’ar samun zaman lafiya – Abdul’aziz Gafasa

Published

on

Shugaban majalisar dokokin jihar Kano Abdul’aziz Garba Gafasa Walin Gaya ya yi kira ga al’ummar jihar Kano dama kasa baki daya a cigaba da yiwa Nijeriya addu’a a yayin da take cika shekara sittin da samun yancin kai.

Shugaban majalisar Abdul’aziz Garba Gafasa ya bayyana hakan a zaman majalisar dokokin jihar Kano na yau Laraba.

Ya ce, “Kamar yadda muke mika bukatun mu a wajen Allah itama Nijeriya ya na da kyau a saka a addu’a domin samun zama lafiya da kwanciyar hankali”. A cewar Abdul’aziz Garba Gafasa

A zaman majalisar na yau dan majalisa mai wakiltal karamar hukumar Bunkure Muhammad Uba Gurjiya ya nemi majalisar da ta yi kira ga gwamnati da ta ci gaba da aikin hanyar dake yankunan su domin ci gaban yankunan dama jihar Kano.

Wakiliyar mu ta majalisa, Khadija Ishaq Muhammad ta rawaito cewar, shima dan majalisa mai wakiltal karamar hukumar Tudun wada, Abdullahi Iliyasu Yaryasa ya nemi majalisar da ta yi kira da gwamnati akan daga darajar wasu asibitoci dake yanki nashi na saboda yanki na kan babban hanya ta zuwa wasu jihojin wanda rashin babban asibitin yana jefa mutanen yankin cikin mawuyacin hali.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending