Connect with us

Labarai

Mutane 14 sun gurfana a kotu kan zargin kisan kai

Published

on

Kotun majistrate mai lamba 18 da ke zaman ta a unguwar Gyadi-gyadi karkashin mai shari’ah Auwal Yusuf Sulaiman, wani mutum mai suna Liman Amadu da ragowar mutane 13 ‘yan garin Chediyar Jajira da ke karamar hukumar Dawakin Tofa ne suka sake gurfana a gaban kotun da sabuwar takardar tuhuma.

A baya dai an gurfanar da su ne da laifin da hada kai wajan aikata laifi da husuma da sanadin haddasa mummunan rauni da kuma ta da gobara.

Da fari dai wata hatsaniya ce a ke zargin ta barke tsakanin ‘yan garin na Chediyar Jajira da kuma na garin Kaburma duk a karamar hukumar ta Dawakin Tofa, har kuma a ke zargin ‘yan garin Chediyar Jajiran sun tsinkewa wani matashi mai aikin asibiti, Adamu Haladu yatsu, lokacin da yaje wucewa, ana kuma tsaka da shari’ar Allah ya yi masa rasuwa.

Dalilin hakan ne a ka mayar da su wajan ‘yan sanda domin sake bincikawa inda su kuma suka sake wata takardar tuhuma ciki har da laifin kisan kai a cikin tuhumar da a ke musu.

Maryam Jibrin ita ce lauyan gwamnati ta kuma roki a karanta musu kunshin tuhumar bayan kuma an karanta din duk sun musan ta, a nan ne kotun ta daga zaman zuwa ranar 12 ga watan 11 domin ci gaba.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewar, wadanda a ke zargin danka su a hannun jami’an gidan ajiya da gyaran hali domin kai su gidan ajiya da gyaran halin.

Labarai

Shugabanni ku fito da sabbin dabaru domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta tsadar rayuwa a ƙasa – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights dake jihar Kano, ta ce akwai buƙatar shugabanni suyi abinda ya dace dan ganin an kawo karshen matsalar tsaro, da kuma ta harkar tsaro dake ci gaba da addabar mutane a sassa ƙasar nan.

Daraktan ƙungiyar Kwamared Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantwarsa da gidan rediyon Dala FM, a ranar Laraba, ya ce yadda ake ƙara samun ƴan ta’adda suna sace mutane tare da kashe su a sassan ƙasar nan, da kuma halin matsin rayuwar da ake fuskanta akwai buƙatar shugabanni suyi abinda ya kamata dan ganin an kawo ƙarshen matsalolin.

“Yawaitar kai hare-haren da ake samu daga ɓangaren ƴan bindiga a cikin al’ummar gari akan kashe su tare da sace su matuƙar ana son a kawo karshen matsalar, sai an ƙara himma wajen samar da makamai ga jami’an tsaro tare da samar da sabbin dabaru domin kawar da matsalar, “in ji Galadanci”.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kaɗan da sako ɗalibai aƙalla su sama da 285, na makarantar Kuriga dake ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, da ƴan bindiga suka sace su a baya, baya ga wasu ɗaliban da aka sace a wata makarantar Tsangaya a jihar ta Kaduna, wanda ko a jihar Borno ma aka jiyo yadda aka sace ƴan gudun hijira da dama a baya-bayan nan, inda matsalolin tsaron ke ƙara yin gaba a sassan ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnan Kano ya kafa kwamitin duba yadda ake rabon tallafin abincin Azumi

Published

on

Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin duba yadda ake ciyarwar azumin watan Ramadan, a kananan hokumomin cikin birnin jihar 8, domin sa ido da duba yadda ake gudanar da aikin dafawa da rabawa al’umma abincin.

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamitin ne ƙarƙashin kulawar mataimakin gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da wasu ƴan kwamitin.

Hakan na zuwa ne dai bayan da gwamna Abba Kabir, ya ziyarci wasu daga cikin wuraren da ake dafa abincin, inda ya nuna rashin jin daɗin sa kan yadda ya ga aikin ke gudana a karamar hukumar kumbotso.

Bayanin hakan ya fito ne ta cikin wata sanarwar da babban mai taimakawa gwamnan Kano, na musamman akan gidajen rediyo Bashir Aminu Fanshekara, ya aikowa manema labarai, ya ce an bayyana Alhaji Danyaro Yakasai, a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin mai mambobi 7.

Fanshekara ya ce kwamitin ya fara zagayawa wasu daga cikin mazaɓu dake karamar hukumar kumbotso, domin duba yadda ake dafawa da kuma raba abincin tallafin ga al’umma, inda suka suka fara da mazaɓar Na’ibawa a ranar Asabar 23 ga watan Maris ɗin shekarar 2024.

Continue Reading

Ilimi

Kaduna:- Daliban Kuriga sun sha ki iskar ‘yanci

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da rahoton cewa an sako duka ɗaliban makarantar Kuriga da ƴanbindiga suka sace.

 

An sace ɗaliban firamare da na sakandare su kusan 287 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna fiye da makonni biyu da suka wuce.

 

Sanarwar da gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya fitar ta ce an sako duka ɗaliban kuma suna cikin koshin lafiya.

 

Sanarwar ba tayi karin bayani ba game da irin matakan da aka bi wajen sako ɗaliban, sai dai gwamna Uba Sani ya nuna godiya ga shugaba Tinubu da mai bashi shawara kan tsaro da kuma sojojin Najeriya saboda irin rawar da suka taka wajen ganin an sako ɗaliban.

 

“Ba dare babu rana ina tattaunawa da Malam Nuhu Ribadu domin lalubo hanyoyin da za a bi wajen kubutar da daliban, kafin mu samu nasara,” in ji Uba Sani.

 

Galibinsu ɗaliban da aka sace ƴan shekaru biyar ne zuwa 18.

Continue Reading

Trending