Connect with us

Labarai

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi holin matasa 242

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi holin wasu matasa su kimanin 242 wadanda ake zargins u da laifuka daban-daban.

Cikin matasan akwai wadanda aka kama da motocin sata da baburan adaidaita sahu na sata da kuma wayoyin sata.

Rundunar ta kuma kama wasu da aka zargin masu garkuwa da mutane ne da ‘yan fashi da makami da kuma dilolin dabar wiwi.

An kuma kama wasu da ake zargin ‘yan damfara ne da wadanda ake zargin su na satar kudaden mutane a na’urar ATM.

Rundunar ta kuma samu nasarar kama wasu bindigogi kirar AK 47 guda tara da alburusai masu tarin yawa, sai kuma wasu tarin wukake da haramtattun kwayoyi da aka kama masu tarin yawa.

An kuma damke wani da ake zargin su na yiwa direbobin Babur din adaidaita kwacen Baburan su.

Rundunar ta kuma kama wani wanda ake zargin ya yanka wani abokin sa amma abokin bai yanku ba.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewar, mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna ya bayyana cewar, su na gamsuwa da hadin kan da al umma su ke ba su.

Labarai

Ganduje ya bayar da umarnin rufe makarantun gaba da Sakandire Uku

Published

on

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umarnin rufe wasu cikin makarantun gaba da Sakandiren jihar nan take.

Hakan na cikin wata sanarwa da Kwamishiniyar ilimi mai zurfi ta jiha Dr. Mariya Mahmud Bunkure ta fitar.

Makarantun da aka rufe sun haɗar da, Kwalejin share fagen shiga jami’a ta Rabi’u Musa Kwankwaso da ke Tudunwada.

Sai kuma Kwalejin nazarin tsaftar muhalli da ke garin Gwarzo, da kuma ta fasahar bunƙasa sana’o’in dogaro da ke garin Rano.

Rufewar ta kuma shafi Kwalejin nazarin harkokin noma da ke garin Ɗanbatta.

Ta cikin sanarwar Kwamishiniyar ta ce, an ɗauki wannan mataki ne sakamakon shawarwarin da aka bai wa Gwamnati, ɗalibai su gaggauta koma wa zuwa gida nan take.

Idan hali ya yi, Kwamishiniyar ta ce, za a sanar da ranar ci gaba da karatun.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu kula da harshe domin guje wa illar sa – Limamin Kuntau

Published

onLimamin masallacin Juma’a na Ashabul Kahfi dake unguwar Kuntau Malam Munzali Bala Koki ya ce, al’umma su rinka kiyaye lafuzan su domin duk abinda mutum ya fada za a yi masa hisabi akan sa.


Malam Munzali ya bayyana hakan ne a hudubar Juma’a da ya gabatar a masallacin Ashabul Kahfi.
Ya na mai cewa, mu rinka kiyaye harshen mu domin kaucewa furta zai kai mu ga yin danasan, idan kuma bakin k aba zai fadi alheri ba to yayi shiru shi ne yafi.


Saurari wannan domin jin cikakken rahoton.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mawadata sai sun rinka tallafawa mabukata – Limamin Sani Mainagge

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Jami’u Amiril Jaishi dake unguwar Sani Mainagge Mukhtar Abdulkadir Dandago ya yi kira ga madata da su rinka taimakawa wadanda ke da bukata ta hanyar ciyarwa da zakka domin samun dacewa da rahmar ubangiji.


Malam ya bayyana hakan ne yayin hudubar Juma’a da ya gabatar a masallacin Juma’a na Jami’u Amiril Jaishi.


Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!