Connect with us

Labarai

#EndSARS: Jihohi biyar aka sanyawa dokar hana fita a Najeriya

Published

on

Jihar Ekiti da ke kudu maso yamma, da kuma Filato da ke tsakiyar arewacin Najeriya ne na baya-bayan nan da suka sanya dokar hana zirga-zirga na tsawon sa’o’i 24 a ranar Talata, bayan an tashi da dokar ta bacin a jihar Lagos.

JIHAR EDO

Jihar Edo ce daga Kudu-maso-Kudu ta fara sanya dokar ta baci, bayan balle gidan yari a Benin da ake zargin masu zanga-zangar sun yi a ranar Litinin.

Gwamnatin Edo ta sanya dokar hana fita har sai abin da hali ya yi, kuma dokar ta soma aiki ne nan take.

Gwamnan jihar, Godwin Nogheghase Obaseki, ya ce matakin sanya dokar ya zama dole ganin yadda fusatattun masu zanga-zangar ke kai hare-hare kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba da sunan zanga-zangar EndSARS.

Yadda aka yi zanga-zanga a Edo

JIHAR LEGAS

A ranar 20 ga watan Oktoban 2020 ne, gwamnan Babajide Sanwo-Olu, ya ayyana dokar hana fita, wadda ta soma aiki da yammacin ranar Talatar.

Amma daga bisani aka sassauta dokar domin bai wa mutanen da suka fita aiki ko kuma wurin sana’a damar komawa gida, kafin dokar ta koma yadda take a baya.

Wannan ya zo ne sakamakon sauya salo da masu zanga-zangar #EndSARS suka yi na tayar da rikici, kamar yadda gwamnan ya bayyana.

Ko da yake gwamna, Sanwo-Olu, ya ce ma’aikatan da ya zama wajibi su fita aiki aka amince a gani a waje.

Amma duk da haka masu zanga-zangar sun bijirewa umarnin gwamnati, inda suka cigaba daga inda suka tsaya, lamarin da ya sanya sojoji suka isa wurin da ake zanga-zangar.

Yadda masu zanga-zanga su ka yi fitar dango a Legas da ke kudancin Najeriya

JIHAR FILATO

Gwamna, Simon Lalong, shima ya sanya dokar hana fita a Kudanci da kuma wasu kananan hukumomi da ke arewacin Jos wadda ta soma aiki daga karfe 8 na daren ranar  Talata.

A wata sanarwa da ya fitar, gwamnan ya ce zanga-zangar da aka fara ta cikin wasu ‘yan kwanaki da suka wuce ta sauya zuwa rikici, bayan da aka samu bata gari suna amfani da zanga-zangar wajen kai hari da kuma cin zarafin jama’a.

An samu mutane cikin masu zanga-zangar da ke ta’adi da kone-konen motoci da farfasa shaguna a titin Ahmadu Bello da kona wani wajen ibada da ke titin Gyero a yankin Bukuru. Sannan akwai mutane 3 da suka mutu. In ji sanarwar

Gwamna Simon Lalong na jihar Filato

JIHAR ABIA

Gwamna Abia Okezie Ikpeazu, shima ya sanya dokar hana fita ta ba dare ba rana a Aba da Umuahia daga karfe 6 na yamma har sai abin da hali ya yi, a wani mataki na kare dukiyoyi da rayukan jama’a.

Wata sanarwa da gwamnan ya fitar ta hannun kwamishinan yada labarai, John Okiyi Kalu,  ya ce ‘yan daba sama da 30 ne suka kaiwa wani ginin ‘yan sanda hari a lokacin zanga-zangar.

 

Masu zanga-zanga a jihar Abia kenan

Sanarwar ta tabbatar da cewa jami’in dan sanda guda ne ya rasa ransa sakamakon harin ‘yan dabar da ke dauke da makamai, inda suka kwace bindigogi da harsashai.

Ko da yake gwamnatin Abia ta ce an cafke mutum guda daga cikin maharan, sakamakon raunin da ya samu daga harbin bindiga.

JIHAR EKITI

Shima dai gwamna, Kayode Fayemi ya bayar da umarnin sanya dokar hana fita, bayan da bata gari suka sauyawa zanga-zangar EndSARS suna zuwa rikici.

Gwamnatin dai ta ayyana dokar hana fita ba dare-ba-rana, wadda ta shafi kowanni bangare a ranar Talata.

Yadda masu zanga-zanga suka fara fitowa a jihar Ekiti

Gwamnan ya bayyana damuwa kan yadda gangamin #EndSARS da aka soma a cikin lumana ya ya ke neman munana a jihar.

Wanne mataki gwamnatin Najeriya ta dauka?

Babban Sifeton ‘yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu, ya bayar da umarnin a baza jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoma a sassan kasar, a wani bangare na shirin ko-ta-kwana.

Sanarwar babban sufeton ‘yan sandan, na zuwa ne bayan samun karuwar tashe-tashen hankula a wasu jihohi sakamakon zanga-zangar neman a rushe rundunar SARS ko kuma SWAT, bayan da aka zargi jami’an sashen da cin zarafin jama’a.

Labarai

Shugabanni ku fito da sabbin dabaru domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta tsadar rayuwa a ƙasa – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights dake jihar Kano, ta ce akwai buƙatar shugabanni suyi abinda ya dace dan ganin an kawo karshen matsalar tsaro, da kuma ta harkar tsaro dake ci gaba da addabar mutane a sassa ƙasar nan.

Daraktan ƙungiyar Kwamared Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantwarsa da gidan rediyon Dala FM, a ranar Laraba, ya ce yadda ake ƙara samun ƴan ta’adda suna sace mutane tare da kashe su a sassan ƙasar nan, da kuma halin matsin rayuwar da ake fuskanta akwai buƙatar shugabanni suyi abinda ya kamata dan ganin an kawo ƙarshen matsalolin.

“Yawaitar kai hare-haren da ake samu daga ɓangaren ƴan bindiga a cikin al’ummar gari akan kashe su tare da sace su matuƙar ana son a kawo karshen matsalar, sai an ƙara himma wajen samar da makamai ga jami’an tsaro tare da samar da sabbin dabaru domin kawar da matsalar, “in ji Galadanci”.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kaɗan da sako ɗalibai aƙalla su sama da 285, na makarantar Kuriga dake ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, da ƴan bindiga suka sace su a baya, baya ga wasu ɗaliban da aka sace a wata makarantar Tsangaya a jihar ta Kaduna, wanda ko a jihar Borno ma aka jiyo yadda aka sace ƴan gudun hijira da dama a baya-bayan nan, inda matsalolin tsaron ke ƙara yin gaba a sassan ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnan Kano ya kafa kwamitin duba yadda ake rabon tallafin abincin Azumi

Published

on

Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin duba yadda ake ciyarwar azumin watan Ramadan, a kananan hokumomin cikin birnin jihar 8, domin sa ido da duba yadda ake gudanar da aikin dafawa da rabawa al’umma abincin.

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamitin ne ƙarƙashin kulawar mataimakin gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da wasu ƴan kwamitin.

Hakan na zuwa ne dai bayan da gwamna Abba Kabir, ya ziyarci wasu daga cikin wuraren da ake dafa abincin, inda ya nuna rashin jin daɗin sa kan yadda ya ga aikin ke gudana a karamar hukumar kumbotso.

Bayanin hakan ya fito ne ta cikin wata sanarwar da babban mai taimakawa gwamnan Kano, na musamman akan gidajen rediyo Bashir Aminu Fanshekara, ya aikowa manema labarai, ya ce an bayyana Alhaji Danyaro Yakasai, a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin mai mambobi 7.

Fanshekara ya ce kwamitin ya fara zagayawa wasu daga cikin mazaɓu dake karamar hukumar kumbotso, domin duba yadda ake dafawa da kuma raba abincin tallafin ga al’umma, inda suka suka fara da mazaɓar Na’ibawa a ranar Asabar 23 ga watan Maris ɗin shekarar 2024.

Continue Reading

Ilimi

Kaduna:- Daliban Kuriga sun sha ki iskar ‘yanci

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da rahoton cewa an sako duka ɗaliban makarantar Kuriga da ƴanbindiga suka sace.

 

An sace ɗaliban firamare da na sakandare su kusan 287 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna fiye da makonni biyu da suka wuce.

 

Sanarwar da gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya fitar ta ce an sako duka ɗaliban kuma suna cikin koshin lafiya.

 

Sanarwar ba tayi karin bayani ba game da irin matakan da aka bi wajen sako ɗaliban, sai dai gwamna Uba Sani ya nuna godiya ga shugaba Tinubu da mai bashi shawara kan tsaro da kuma sojojin Najeriya saboda irin rawar da suka taka wajen ganin an sako ɗaliban.

 

“Ba dare babu rana ina tattaunawa da Malam Nuhu Ribadu domin lalubo hanyoyin da za a bi wajen kubutar da daliban, kafin mu samu nasara,” in ji Uba Sani.

 

Galibinsu ɗaliban da aka sace ƴan shekaru biyar ne zuwa 18.

Continue Reading

Trending