Connect with us

Addini

Zumunci na kawo budi a rayuwa – Malam Lawi

Published

on

Malamin addinin Islama dake Kano, Mallam Lawi Sunusi Paki, ya ce al’ummar musulmai da su ƙara ƙaimi wajen sada zumunci, domin rabauta da rahamar Allah (S.W.T) a nan duniya da ma gobe ƙiyama.

Mallam Lawi Paki ya bayyana hakan ne a yayin taron Maulidin Manzon Allah (S.A.W) wanda matasan Ja’en Gidan Wakili dake yankin ƙaramar hukumar Gwale suka gabatar a unguwar a ranar Laraba.

Ya na mai cewar,”Matuƙar musulmai za su rinƙa sada zumuncin a tsakanin su, haƙiƙa za su samu wani buɗi a cikin rayuwar su ta yau da kullum. Su ma waɗanda a ke kaiwa ziyarar, su daina sanya tunanin za a ba su wani abun, domin hakan ya na sanyawa masu niyyar sada zumuncin tsoro a zuƙatan su, kuma ba koyarwar Ma’aiki (S.A.W) ba ce”. Inji Mallam Lawi.

Da yake nasa jawabin jagora a taron Maulidin, Mallam Shamsudden Ibrahim, miƙa godiyar sa ya yi ga dukkanin waɗanda suka halarci taron Maulidin ya yi.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar, al’umma da dama ne dai suka samu damar halartar taron Maulidin Ma’aikin (S.A.W). maza da mata manya da yara, kuma matasan suna gabatar da Maulidin ne duk shekara-shekara a irin wannan wata na Rabi’ul Auwal.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Addini

Tijjani Gandu: Mawakan yabo su kaucewa fadin kalmomi marasa amfani

Published

on

Mawaki Ahmad Tijjani wanda a ka fi sani da suna Tijjani Gandu, ya ja kunnen ‘yan uwan sa mawaka musamman ma na yabo da su kaucewa yin wakokin da za su jefa kalmomin da ba su da ce ba ga fiyayyen halita.

Tijjani Gandue ya ce ma su wakokin yabo da za su rinka tambaya kafin su rubuta tare da raira waka, da tuni an tsaftace wakokin yabo.

Mawakin na wadan nan kalaman ne a lokacin da makarantar Zawiyyatut Tijjaniyya Al Harazimiyyah ta yi taron Maulidin ma’aiki S.A.W, wanda a ka yi a unguwar Gandun Albasa dake jihar Kano a daren Alhamis.

Ya na mai cewa,”Matukar mawakan yabon za su rinka tambaya da kiyaye kalaman su a cikin wakokin yabon da su ke yi, babu shakka za su samu nasarori a cikin wakokin na su”. Inji Tijjani Gandu.

Da yake nasa jawabin shugaban makarantar Mallam Kabiru Adam Gandun Albasa, mika godiyar sa ya yi ga dukkanin wadanda su ka halarci taron Maulidi ya yi, sannan kuma ya yi kira ga iyaye da su kara kulawa da karatun ‘ƴa’ƴan su, domin rayuwar su ta zama abar alfahari a nan duniya dama gobe kiyama.

Wakilin Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Mallam Kabiru Adam shi kuwa kira ya yi ga dalibai, da su tashi tsaye wajen neman ilimin addini da na zamani, domin kaucewa zaman duhun dukununu.

Continue Reading

Addini

Kano: Mun bayar da kwana 40 a mayar da almajirai gidajen su – Dr. Zahra’u

Published

on

Gwamnatijn Jihar Kano za ta fara kwashi almajirai da ke barace-barace a kan Shatale-tale, da mahadar tituna a fadin jihar Kano tare da bai wa alaranmomin wa’adin kwanaki Arba’in, da su mayar da almajiaran su gidajen su.

Kwamishiniyar harkokin mata da kananan yara ta Jihar kano Dr. Zahra’u Muhammad Umar ce ta bayana hakan a wani taron manema labarai a ranar Laraba.

Ta ce, “Daukan wannan mataki ya zama dole sakamakon bayanan sirri da gwamnati ke samu na yin lalata da wasu yara mata da a ke zargin mabarata ne”.

Ta kuma ce, “A bangaren kananan al’amajirai kuwa gwamnati ta bai wa alaranmomin su kwanaki Arba’in domin mayar da su gidajen su”. A cewar Dr. Zahra’u Muhammad

Wakiliyarmu Yusuf Ali Abdullah ya ruwaito cewa, gwamnatin ba za ta saurarawa duk alaranmomin da suka bujirewa umarninta ba.

Continue Reading

Addini

Rahoto: An fara sallah a masallacin Juma’a na Yamadawa

Published

on

An bude sabon masallacin Jum’a a unguwar Yamadawa, Dorayi Babba da ke karamar Hukumar Gwale a jihar Kano, wanda a ka sakawa suna Masjidul Su’ada.

Hudubar da Limamin masallacin, Muhammad Hadi Sarki ya gabatar ta kunshi kiran al’umma da yin Istigfari domin neman gafarar ubangiji.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!