Connect with us

Labarai

Ci gaban ilimi: Tsoffin dalibai su rinka tallafawa makarantu – Sarkin Kano

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce, dole ne sai tsoffin dalibai sun taimakawa bangaren ilimi a kasar nan, la’akari da yadda gwamnatin kadai ba za ta wadatar ba.

Sarkin na Kano na bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wajen taron bikin cika shekara 30 na tsoffin daliban makarantar ‘yan mata ta Sumaila SOGA aji na 1990.

Sarkin wanda Fagacin Kano Alhaji Habibu Bello Dankadai ya wakilta, ya bukaci tsoffin daliban na Sumaila da su rika taimakawa makarantar tasu da ta fannin ci gabanta domin tabbatar da samun ilimi mai nagarta ga daliban yanzu.

Shugabar kungiyar Hajiya Halima Ibrahim ta ce, “Dama kudirin kungiyar mu shi ne mu tallafawa makarantar, wanda tuni muka rafa tallafawa makarantar da gyaran wasu sassanta da kuma kayan koyo da koyarwa”. A cewar Hajiya Halima Ibrahim.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Rahoto: Mu na bukatar gyaran titi a yankin mu – Unguwar Jakada

Published

on

Al’ummar Dorayi Babba unguwar Jakada sun yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta gyara musu Titin da ya tashi daga unguwar ta Jakada zuwa Rijiyar Zaki Tasha, domin ci gaba da jin dadin zirga-zirgar ababen hawa.

Al’ummar yankin sun yi kiran ne a yayin zantawar su da wakilin mu Tijjani Adamu a ranar Laraba.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rundunar ƴan sandan Kano ta cafke matashi da sinƙi-sinƙin tabar wiwi

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta cafke wani matashi a unguwar Ɗanbare ɗauke da sinƙi-sinƙin tabar wiwi, da aka sarrafa tamkar sinƙin Biredi.

Matashin ya ce, wiwin ta mahaifinsa ce, kuma yanzu an kama shi, hakan ya sa mahaifiyarsa ta umarce shi da ya sauya wa tabar wuri.

A cewar sa, mahaifin na sa ya shafe sama da shekara ashirin yana sana’ar safarar tabar wiwin.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, sun cafke matashin ne ta hanyar bayanan sirri da suka samu.

Kiyawa ya ce, tuni aka mayar da lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar ƴan sandan Kano.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin Kano za ta sauyawa gidan Zoo matsuguni

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, za ta sauya wa gidan adana namun daji na jihar matsuguni.

Kwamishinan raya al’adu da kayan tarihi na jihar Kano Ibrahim Ahmad ne ya shaida wa Freedom Radio hakan.

Kwamishinan ya ce, dalilin wannan sauyi shi ne, gidan adana namun dajin ya yi kusa da jama’a, kuma dabbobin ba sa son hayaniya.

A cewar sa, za a mayar da gidan adana namun dajin zuwa garin Tiga da ke ƙaramar hukumar Bebeji.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!