Connect with us

Labarai

Rahoto: Direban adaidaita sahu da ya gudu da kayan fasinjoji ya shiga hannu

Published

on

Wani direban adaidaita sahu da ya gudu da kayan wasu fasinjoji mata a unguwan Na’ibawa bayan ya bukaci su sauka su tari daga cikin baburin nasa su tura shi, yana tashi kuma sai ya gudu da kayan su.

Matan sun yi kokarin daukar lambar baburin adaidaita sahun, kuma suka garzaya ofishin ‘yan sanda sukanar da jami’an sanda inda suka fara bincike daga bisani kuma suka samu nasarar kama shi.

Saurari Abba Isah Muhammad domin jin cikakken rahoto.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Rahoto: Rashin kula da tarbiyar yara kan sanya su lalacewa – Malami

Published

on

Wani malamin makaranta a jihar Kano Malam Nasir Ghali Mustapha ya ce, rashin daukar ‘ya’ya da mahimmanci a wannan zamani kan sanya yara lalacewa.

Malam Nasir Ghali ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu Tijjani Adamu.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Zargin kisan kai: Kotu za ta fara sauraron shaidu watan gobe

Published

on

Babbar kotun jiha mai lamba 9 karkashin mai shari’a Aisha mahamud ta sanya ranar 9 ga watan gobe domin fara sauraron shaidu cikin kunshin tuhumar da gwamnatin Kano ke yiwa wasu matasa 3 da ake zargin su da hallaka wani matashi a unguwa uku.

Kunshin zargin ya bayyana cewar matasan sun hada baki da wasu mutane 6 wadanda a yanzu sun tserewa shari’a  sun hallaka wani matashi mai suna Shamsu Yakubu ta hanyar caka masa wuka a kirji .

Matasan da aka gurfanar sun hadar da Aminu Malan da Martin Joseph da kuma Tahir Tanimu.

Sai dai dukkanin su sun musanta zarge-zargen, lauyan gwamnati Lamido Sorondinki ya bayyanawa kotun cewar za su gabatar da shaidu.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Yadda NDLEA ta yi holin kayan maye a Kano

Published

on

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Kano NDLEA ta yi holin kayan mayen da ta kama daban-daban.

Kwamandan hukumar a jihar Kano Dr Ibrahim Abdul ne ya bayyana hakan yayin da yake bayani a kan mutanen da suka kama da nau’ikan kayan maye daban-daban.

Saurari Abba Isah Muhammad domin jin cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!