Connect with us

Labarai

Mu na aiki fiye da sauran Hukumomin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya – Muhyi Magaji

Published

on

Shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa na jihar Kano Barrister Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce, hukumar sa na aikin yaki da cin hanci da rashawa fiye da wasu hukumomin cin hanci da rashawa a Najeriya.

Barrister Muhyi Magaji Rimin Gado ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, lokacin da ake bikin ranar yaki da cin hanci da rashawa tare da kaddamar da cibiyar horarwa kan yaki da cin hanci da rashawa a jihar Kano.

Ya ce, “Mun samu nasara ne a hukumar ne sanadiyyar rashin shiga aikin mu wajen yaki da cin hanci da rashawa da gwamnati ke yi, tare da samun goyon baya wajen yaki da cin hanci da rashawa a jihar Kano”. A cewar Barrister Muhyi Magaji Rimin Gado.

Da yake jawabi gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce, gwamnatin jihar Kano za ta ci gaba da baiwa hukumar kwarin gwiwa wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Gwamna Ganduje da ya samu wakilcin mataimakin sa Nasir Yusif Gawuna wanda ya kara da cewa, duba da yadda matsalar cin hanci da rashawa ke dakile tattalin arzikin kasa ya zama lallai gwamnatin ta ci gaba da marawa hukumar baya wajen ayyukanta.

Wakiliyar mu Zahra’u Nasir ta rawaito cewa, a yayin taron na ranar Laraba masu ruwa da tsaki da dama akan yaki da cin hanci da rashawa da dama ne suka halarci taron.

 

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending