Connect with us

Manyan Labarai

PDP: Mun kori Kwankwaso daga jam’iyar – Aminu Wali

Published

on

Jam’iyyar PDP tsagin Alhaji Aminu Wali ta bayyana dalilan ta a kan korar tsohon gwamnan Kano, Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso daga jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar, Munhaminna Baƙo Lamiɗo ne ya sanar da korar Kwankwaso a ranar Alhamis, bayan babban taron jam’iyyar na jiha.

Lamiɗo ya ce,”An dakatar da shi ne saboda zargin yi wa jam’iyyar zagon ƙasa, da kuma haɗa baki da jam’iyya mai ci a matakin ƙasa, domin samun takara a 2023. Haka kuma Kwankwason ya haifar da baƙin jini da ƙiyayya a tsakanin ƴan jam’iyyar PDP wanda ya haifar da asarar ɗan majalisar tarayya Ali Datti Yako. Kwankwason ya na karya dokokin jam’iyyar tare da ƙin biyayya ga kwamitin zartarwa na jam’iyyar a Kano. Sannan Kwankwaso ya na cin zarafi tare da wulaƙanta shugabannin jam’iyyar na jiha”. Inji Munhaminna.

Sai dai jam’iyyar PDP tsagin Kwankwaso ba ta ce komai ba dangane da wannan batun.

Labarai

Rahoto: Ina zargin mai sayar da fili ya bani takardar Biredi – Wata Mata

Published

on

Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu, wata mata ta yi karar wani mutum da cinye mata Filaye guda takwas ta hanyar ba ta takardun bogi.

Sai dai kafin fara shar’ar ne kotun ta samu sanarwar dakatar da gudanar da shari’a saboda hutu da kotunan jihar Kano su ka tafi a ranar ta Talata.

Saurari wannan domin jin cikakken rahoton.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Kotunan jihar Kano na jiran umarnin tafiya hutu a rubuce – Baba Jibo

Published

on

Mai magana da yawun kotunan jihar Kano Baba Jibo Ibrahim ya tabbatar da umarnin rufe kotunan jihar Kano a ranar Talata.

Sai dai Baba Jibo Ibrahim a yayin zantawarsa da wakilin Ibrahim Abdullah Sorondinki ya ce, suna jiran umarnin ne a rubuce domin sanar da kotuna da kuma sauran al’umma akan halin da ake ciki.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: ‘Yar kasuwa ta gurfana a kotu kan zargin cinye manyan Kudade

Published

on

Babbar kotun shari’ar musulunci da ke filin Hockey karkashin mai shari’a Abdullahi Halliru Abubakar, ta gurfanar da wata mata kan zargin karbar kudi Naira miliyan tara da dubu dari shida a hannun wani mutum da zummar za su yi harkar kasuwancin Dala.

Mutumin mai suna Musa Yusuf Abubakar yana karar matar mai suna Farida Usman Dantata, da cinye kudaden, wanda kuma kasancewar ranar Talatar hutu a ke yi mai shari’a bai zo ba, aka dage shari’ar zuwa ranar biyu ga watan uku shekarar 2021.

Domin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!