Addini
Matasa: Mu kara kaimi wajen halartar sallar Jana’iza – DR Abdallah

Limamin masallacin juma’a na Usman Bin Affan dake unguwar Gaɗan Ƙaya, Dr Abdallah Usman Umar, ya yi kira ga al’ummar musulmai da su ƙara ƙaimi wajen halartar sallar Gawa yayin da a ka yi mutuwa bisa amfanin ta.
Dr Abdallah ya yi kiran ne ta cikin shirin Rayuwa abar koyi na gidan rediyon Dala, wanda ya gudana da safiyar Juma’a.
Ya na mai cewa”Matuƙar al’ummar musulmai za su ƙara ƙaimi wajen halartar Sallar Jana’izar, babu shakka za su rabauta da rahmar Allah (S.W.T) a nan duniya dama ranar gobe ƙiyama. Bai kamata mutane su rinƙa sallar jana’izar ta na wuce su ba, bisa ladan da Allah (S.W.T) ya ke bayarwa ga dukkanin wanda ya yi, sannan su rinƙa kasancewa cikin nutsuwa a yayin da su ke gudanar da dukkanin sallolin da su ke yi na yau da kullum”. inji Dr. Abdallah.
Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Dr Abdallah Usman Umar, ya kuma shawarci al’umma da su dage wajen sanin yadda ake sallar jana’izar domin wata rana zasu iya tsintar kansu wajen jagorantar sallar jana’izar idan anyi.
Addini
Rahoto: Wajibi ne mu martaba ahalin Manzo (S.A.W) – SP Abdulkadir

Limamin masallacin Juma’a na Shalkwatar rundunar ‘Yan sanda dake Bompai, ya ce wajibi ne a martabar ahalin fiyayyen halita da sahaban sa.
SP Abdulkadir Haruna, ya kuma ce al’umma su kasance masu zaman lafiya a ko da yaushe.
Wakilin Mu Abba Isah Muhammad daga masallacin ya turo mana da rahoto.
Addini
Rahoto: Yin ayyuka na gari zai kai mutum tudun mun tsira – Mal. Ahmad

Na’ibin masallacin Juma’a Quba dake Tukuntawa a karamar hukumar Tukuntawa, Ahmad Muhammad Ali, ya ce ayyuka na gari su ne za su sa dan Adam ya tsira a rayuwar duniya.
Ahmad Muhammad Ali, ta cikin hudubar shi da ya yi a Juma’ar nan, ya ce mutum ya guji yin shirka da sabawa iyaye, domin rabauta da gidan Aljanna.
Ga wakilin mu Ibrahim Abdullahi Sorondinki, daga masallacin na Masjid Quba da rahoto.
Addini
Rahoto: Karbar cin hanci zai kai mutum zuwa wuta – Dr Abdullahi

Babban limamin masallacin Juma’a na Umar Sa’id Tudun Wada, Dr Abdullahi Jibril Ahmad, ya ce duk wanda ya karbi cin hanci ya sani cewa zai hadu da fushin Allah a ranar Kiyama.
Dr Abdullahi Jibril Ahmad ta cikin hudubar shi da ya gabatar a yau, ya ce Manzon Allah S.A.W ya ce dukannin wata tsoka da ta ginu daga cin hanci, za ta shiga wuta, kuma idan mutum ya na karbar cin hanci za a dauke masa dukannin albarka a rayuwar shi da ta iyalan shi.
Ga cikakken rahoton da wakilin mu Tijjani Adamu ya turo mana daga masallacin.
-
Manyan Labarai1 year ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi1 year ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai1 year ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi1 year ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai5 months ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi1 year ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai1 year ago
Ba’amurkiya da masoyin ta sun hada cinkoso a kasuwar Sabon Gari
-
Manyan Labarai1 year ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano