Connect with us

Labarai

KAROTA: An kama mai Safarar tabar wiwi zuwa Kano

Published

on

Hukumar KAROTA ta cafke wani mutum mai suna Mista Ekennah Okechuku wanda ya yi safarar Sinki 60  na tabar wiwi zuwa jihar Kano.

Hakan na cikin wata takarda mai dauke da Sa hannun mai magana da yawun hukumar KAROTA Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa aka kuma rabawa manema labarai.

Sanarwar ta kuma ce, wanda aka kama Mista Ekennah Okechuku ya na cikin jerin sunayen mutanen da hukumar NDLEA ta ke nema.

Sai dai yayin mika wanda ake zargin ga Kwamandan, NDLEA, shugaban hukumar KAROTA, Hon. Baffa Babba Dan Agundi ya bayyana cewar, kwanan nan hukumar ta ba da umarnin sauyawa tashar motoci ta Sabon Gari matsuguni saboda rahoton irin laifukan da ake aikatawa da irin wadannan motoci.

Baffa Babba, ya kuma yi gargadin cewa, duk kamfanin da aka samu direban shi ko yaron shi da laifin hada baki da wasu marasa kishi domin aikata laifi a jihar, za a kama motar kuma a kori kamfanin daga jihar.

Da yake jawabi, Kwamandan, NDLEA, na Kano, Dakta Ibrahim Abdul ya nuna godiya ga hukumar KAROTA kan hadin kai da ke ake samu tsakanin juna na kama masu laifi.

Wanda ake zargin wanda ya fito daga jihar Imo tuni ya amsa laifinsa inda ya bayyana cewa ya na safarar magungunan daga Lagos zuwa Kano inda yake kai wa kwastomomin sa.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending