Connect with us

Labarai

Sai an hada kai da masarautu za a magance matsalar tsaro a Najeriya – Sarkin Alkaluman Kano

Published

on

Sarkin Alkaluman Kano Alhaji Ilyasu Labaran Daneji ya ce matukar hukumomin tsaro a Najeriya suna san kawo karshen matsalolin rashin tsaro a yankin Arewa ya zama wajibi su hada kai da masu rike da masarautun gargajiya.

Ilyasu Labaran Daneji ya bayyana haka ne a yayinda yake zantawa da gidan rediyon Dala a ranar Litinin.

Ya ce, “Hukumomin tsaron kasar nan su sani cewa, ana fama da rashin tsaro la’akari da irin yadda hare- haren ‘yan bindiga ke cigaba da samun wajen zama a yankin, dole ne gwamnati ta sake nazari akan lamarin”. A cewar sarkin Alkaluman Kano.

Ilyasu Labaran Daneji ya nanata cewa, kamata ya yi a yiwa kundin tsarin mulkin kasar nan gyara domin a baiwa masu rike da masarautun gargajiya cikakkiyar dama cikin dokokin tsaron kasa domin hakan zai taimaka wajen samun tsaro.

Haka kuma ya ce, idan gwamnatin tarayya ta dauki wadannan sabbin matakai babu makawa za’a samu sassaucin matsalolin rashin tsaro da yake addabar yankunan Arewacin Najeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Rahoto: Ina zargin mai sayar da fili ya bani takardar Biredi – Wata Mata

Published

on

Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu, wata mata ta yi karar wani mutum da cinye mata Filaye guda takwas ta hanyar ba ta takardun bogi.

Sai dai kafin fara shar’ar ne kotun ta samu sanarwar dakatar da gudanar da shari’a saboda hutu da kotunan jihar Kano su ka tafi a ranar ta Talata.

Saurari wannan domin jin cikakken rahoton.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Kotunan jihar Kano na jiran umarnin tafiya hutu a rubuce – Baba Jibo

Published

on

Mai magana da yawun kotunan jihar Kano Baba Jibo Ibrahim ya tabbatar da umarnin rufe kotunan jihar Kano a ranar Talata.

Sai dai Baba Jibo Ibrahim a yayin zantawarsa da wakilin Ibrahim Abdullah Sorondinki ya ce, suna jiran umarnin ne a rubuce domin sanar da kotuna da kuma sauran al’umma akan halin da ake ciki.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: ‘Yar kasuwa ta gurfana a kotu kan zargin cinye manyan Kudade

Published

on

Babbar kotun shari’ar musulunci da ke filin Hockey karkashin mai shari’a Abdullahi Halliru Abubakar, ta gurfanar da wata mata kan zargin karbar kudi Naira miliyan tara da dubu dari shida a hannun wani mutum da zummar za su yi harkar kasuwancin Dala.

Mutumin mai suna Musa Yusuf Abubakar yana karar matar mai suna Farida Usman Dantata, da cinye kudaden, wanda kuma kasancewar ranar Talatar hutu a ke yi mai shari’a bai zo ba, aka dage shari’ar zuwa ranar biyu ga watan uku shekarar 2021.

Domin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!