Labarai
Rahoto: Matashi ya gurfana a kotu kan zargin satar motoci 3

Kotun majistret mai lamba 14 da ke rukunin kotunan majstret da ke unguwar Gyadi-gyadi, an gurfanar da wani matashi da ake zargin shi da laifin hada baki wajen satar motoci guda uku.
Mai tashin mai suna Isma’il mazaunin Hotoro Tishama, ana zargin sun sace motocin tare da wasu mutane hudu wadanda suka tsere.
Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.
Labarai
Rahoto: Ina zargin mai sayar da fili ya bani takardar Biredi – Wata Mata

Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu, wata mata ta yi karar wani mutum da cinye mata Filaye guda takwas ta hanyar ba ta takardun bogi.
Sai dai kafin fara shar’ar ne kotun ta samu sanarwar dakatar da gudanar da shari’a saboda hutu da kotunan jihar Kano su ka tafi a ranar ta Talata.
Saurari wannan domin jin cikakken rahoton.
Labarai
Rahoto: Kotunan jihar Kano na jiran umarnin tafiya hutu a rubuce – Baba Jibo

Mai magana da yawun kotunan jihar Kano Baba Jibo Ibrahim ya tabbatar da umarnin rufe kotunan jihar Kano a ranar Talata.
Sai dai Baba Jibo Ibrahim a yayin zantawarsa da wakilin Ibrahim Abdullah Sorondinki ya ce, suna jiran umarnin ne a rubuce domin sanar da kotuna da kuma sauran al’umma akan halin da ake ciki.
Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.
Labarai
Rahoto: ‘Yar kasuwa ta gurfana a kotu kan zargin cinye manyan Kudade

Babbar kotun shari’ar musulunci da ke filin Hockey karkashin mai shari’a Abdullahi Halliru Abubakar, ta gurfanar da wata mata kan zargin karbar kudi Naira miliyan tara da dubu dari shida a hannun wani mutum da zummar za su yi harkar kasuwancin Dala.
Mutumin mai suna Musa Yusuf Abubakar yana karar matar mai suna Farida Usman Dantata, da cinye kudaden, wanda kuma kasancewar ranar Talatar hutu a ke yi mai shari’a bai zo ba, aka dage shari’ar zuwa ranar biyu ga watan uku shekarar 2021.
Domin cikakken rahoton saurari wannan.
-
Manyan Labarai11 months ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi1 year ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai11 months ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi1 year ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai12 months ago
Ba’amurkiya da masoyin ta sun hada cinkoso a kasuwar Sabon Gari
-
Nishadi1 year ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Labarai3 months ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Manyan Labarai12 months ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
You must be logged in to post a comment Login
You must log in to post a comment.