Connect with us

Labarai

Mata da miji: Kotu ta fara sauraron kara kan raba auren su

Published

on

Kotun shari’ar Musulinci dake Kofar Kudu karkashin mai shari’a Halhalatul Khuza’i ta fara sauraron karar wata mace dake neman kotu ta raba auren ta da mijinta sakamakon guduwa da ya yi yabar ta watanni goma sha daya baci ba sha.

Matar ta shaidawa kotu cewa, ya gudu yabar ta da ‘yaya hakan yasa ta daukin matakin zuwa kotu domin a raba auren.

Guda cikin madaura auren nasu mai suna Alhaji Gambo ya shaidawa kotu cewa, Salihu ya ci kudin mutane masu yawa hakan yasa shi tserewa saboda kada a kama shi.

A yayin zaman kotun na ranar Laraba mai shari’a Halhatul Khuza’i bayan ya kammala sauraron bangarorin biyu ya bukaci matar da ta kawowa kotu shaidu biyu wadanda za su tabbatar mata cewa, tabbas mijinta ya gudu yabar ta ba ci ba sha tsahon wata goma sha daya.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya rawaito cewa, mai sharia Halhalatul Khuza’i ya sanya ranar goma sha bakwai ga watan Fabarairun sabuwar shekarar da muke ciki domin ci gaba da sauraron shari’ar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Rahoto: Ina zargin mai sayar da fili ya bani takardar Biredi – Wata Mata

Published

on

Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu, wata mata ta yi karar wani mutum da cinye mata Filaye guda takwas ta hanyar ba ta takardun bogi.

Sai dai kafin fara shar’ar ne kotun ta samu sanarwar dakatar da gudanar da shari’a saboda hutu da kotunan jihar Kano su ka tafi a ranar ta Talata.

Saurari wannan domin jin cikakken rahoton.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Kotunan jihar Kano na jiran umarnin tafiya hutu a rubuce – Baba Jibo

Published

on

Mai magana da yawun kotunan jihar Kano Baba Jibo Ibrahim ya tabbatar da umarnin rufe kotunan jihar Kano a ranar Talata.

Sai dai Baba Jibo Ibrahim a yayin zantawarsa da wakilin Ibrahim Abdullah Sorondinki ya ce, suna jiran umarnin ne a rubuce domin sanar da kotuna da kuma sauran al’umma akan halin da ake ciki.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: ‘Yar kasuwa ta gurfana a kotu kan zargin cinye manyan Kudade

Published

on

Babbar kotun shari’ar musulunci da ke filin Hockey karkashin mai shari’a Abdullahi Halliru Abubakar, ta gurfanar da wata mata kan zargin karbar kudi Naira miliyan tara da dubu dari shida a hannun wani mutum da zummar za su yi harkar kasuwancin Dala.

Mutumin mai suna Musa Yusuf Abubakar yana karar matar mai suna Farida Usman Dantata, da cinye kudaden, wanda kuma kasancewar ranar Talatar hutu a ke yi mai shari’a bai zo ba, aka dage shari’ar zuwa ranar biyu ga watan uku shekarar 2021.

Domin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!