Connect with us

Labarai

An dage shari’ar da ake zargin matasa 4 da yunkurin kisa

Published

on

Kotun Majistare mai lamba 54 da ke Nomansland a unguwar Sabon Gari karkashin mai Shari’a, Ibrahim Mansir, ta fara sauraron karar da a ka gurfanar da wasu matasa 4 da laifin kutse cikin gidan Yusira Mal. Zakari mai ‘yan mari dake unguwar Guringawa a karamar hukumar Kumbotso.

A na zargin matasan da raunata ta tare da awon gaba da Motar ta kirar Vibe wanda jami’an ‘yan sanda su ka yi nasarar samun motar a hannun su.

Lauyan Gwamnati mai gabatar da kara, Barrista Aminu Kawo ya karanto kunshin tuhumar da a ke yi wa Aminu M Bello mazaunin Kaduna da Abubakar Hassan da Yusuf Lawan da Yahaya Salisu mazaunin unguwar Sabuwar Gandun a karamar hukumar Kumbotso da laifin hada kai da aikata laifin fashi da makami da yinkurin kisan kai.

Sai dai duakkanin su sun musanta zargin da a ke yi mu su. Amma mai Shari’a, Ibrahim Mansir ya umarci ma’aikatan gidan ajiya da gyaran hali da su tisa keyar su zuwa gidan gyaran hali har sai ranar 11 ga watan 2 na wannan shekarar da muke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Rahoto: Ina zargin mai sayar da fili ya bani takardar Biredi – Wata Mata

Published

on

Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu, wata mata ta yi karar wani mutum da cinye mata Filaye guda takwas ta hanyar ba ta takardun bogi.

Sai dai kafin fara shar’ar ne kotun ta samu sanarwar dakatar da gudanar da shari’a saboda hutu da kotunan jihar Kano su ka tafi a ranar ta Talata.

Saurari wannan domin jin cikakken rahoton.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Kotunan jihar Kano na jiran umarnin tafiya hutu a rubuce – Baba Jibo

Published

on

Mai magana da yawun kotunan jihar Kano Baba Jibo Ibrahim ya tabbatar da umarnin rufe kotunan jihar Kano a ranar Talata.

Sai dai Baba Jibo Ibrahim a yayin zantawarsa da wakilin Ibrahim Abdullah Sorondinki ya ce, suna jiran umarnin ne a rubuce domin sanar da kotuna da kuma sauran al’umma akan halin da ake ciki.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: ‘Yar kasuwa ta gurfana a kotu kan zargin cinye manyan Kudade

Published

on

Babbar kotun shari’ar musulunci da ke filin Hockey karkashin mai shari’a Abdullahi Halliru Abubakar, ta gurfanar da wata mata kan zargin karbar kudi Naira miliyan tara da dubu dari shida a hannun wani mutum da zummar za su yi harkar kasuwancin Dala.

Mutumin mai suna Musa Yusuf Abubakar yana karar matar mai suna Farida Usman Dantata, da cinye kudaden, wanda kuma kasancewar ranar Talatar hutu a ke yi mai shari’a bai zo ba, aka dage shari’ar zuwa ranar biyu ga watan uku shekarar 2021.

Domin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!