Connect with us

Labarai

Masana’antu: Ku yi amfani da damar da aka baku – Ganduje

Published

on

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci masu masana’antun da suka durkushe a jihar da su yi amfani da damar da kungiyoyin bunkasa tattalin arziki suka ba su na bullo da shirin ba da tallafi domin farfado da masana’antunsu.

Gwamnan ya yi bukaci hakan a ranar Litinin yayin taron hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki kan bunkasa tattalin arziki da ya gudana a fadar gwamnatin Kano.

Ya ce, “Gwamnatin Kano ta na yin iya bakin kokarinta domin gayyato kamfanonin samar da wutar lantarki da nufin zuba jari domin samar da tsayayyiyar wutar lantarki a jihar  wajen farfado da masana’antu”.

Ya kuma ce, “Wannan taro zai taimaka wajen jin matsalolin masu masana’antu da nufin samo hanyoyin da za a farfado da su”. A cewar Ganduje.

Tun da farko da take jawabi, Babbar Darakta mai kula da hukumar zuba hannun jari a cikin gida da kasashen waje wato, Hajiya Hama Ali Aware.

Ta ce, babban bankin kasa ya ba da tallafin naira miliyan dubu 10 dan raba wa masanaantu 50 wadanda suka durkushe dan farfado da su su cigaba da aiki kamar yadda ya kamata

Wakiliyar mu Zahra’u Nasir ta rawaito cewa, a yayin taron an Kuma tattauna Kan yadda zaa farfado da masanaantu da suka durkushe sakamakon Corona.

 

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending