Connect with us

Labarai

Hukumar CPC da hadin gwiwar KAROTA sun rufe Kamfanoni 4 a Kano

Published

on

dan KAROTA ya rasa ransa abakin aiki

Hukumar kare hakkin masu Sayayya ta Jihar Kano CPC tare da hadin gwiwar Hukumar KAROTA sun rufe Kamfanoni 4 dake  kan Titin Zungeru Kwakwaci, karamar hukumar Fagge a jihar Kano kan laifuka daban-daban  a ranar Litinin.

Hakan na cikin wata takarda da aka rabawa manema labarai mai dauke da Sa hannun mai Magana da yawun hukumar ta KAROTA Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa a ranar Talata.

Sanarwar ta ce, Hukumomin sun kai simame harabar Kamfanonin bayan da suka tattara ingantattun bayanai cewa, suna aiki da kuma samar da kayayyaki a cikin jihar ba tare da lambar Rajistar NAFDAC ba, da kuma rashin izini daga Ma’aikatar Kasuwanci ta Jihar, da kuma Hukumar kashe gobara ta jihar, yayin da sauran laifukan sun hada da gudanar da irin wadannan Kamfanoni a wuraren zama da kuma ƙin kafa allon alamu.

Sanawar ta kuma kara da cewa, A yayin samamen, Hukumomin sun kuma gano wani gini da aka yi amfani da shi wajen kera wani abu mai hatsari Angur (Snuff) wanda aka yi amannar na da hadari ga lafiyar wadanda ke shakar sa.

A jawabinsa jim kadan bayan aikin, mai rikon mukamin Manajan Darakta, na hukumar Kare Masu Amfani da Masana’antu ta jihar Kano kuma shugaban Hukumar KAROTA Hon. Baffa Babba Dan Agundi wanda ya sami wakilcin Babban mataimaki na musamman ga Gwamna kan KAROTA I, Hon. Nasiru Usman Na’ibawa ya ce, dalilin kai samamen shi ne don tabbatar da Kamfanoni da sauran ‘Yan Kasuwa a cikin Jiha suna aiki bisa ka’idoji domin kaucewa haramtaccen kasuwanci da siyar da sauran kayayyaki marasa kyau.

Usman ya yi gargadin cewa, duk wani kamfani da ke aiki a cikin jihar ba tare da shaidar izini ba kamar yadda dokokin Majalisar suka tanada zai fuskaci hukunci kamar yadda doka ta tanadar.

Ya yi kira ga jama’a da su bai wa hukumar KAROTA bayanan da suka dace a kan duk wani haramtaccen kasuwanci ko Kamfani a cikin jihar domin daukar matakan gaggawa domin kare lafiyar al’umma.

 

Labarai

Ƙudurin gyaran dokar gudanarwar Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi ya tsallake karatu na ɗaya a majalisar dokokin Kano

Published

on

Ƙudurin gyaran dokar gudanarwar Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke jihar Kano, ya tsallake karatu na ɗaya a zauren majalisar dokokin jihar.

Ƙudurin ya kai wannan mataki ne yayin zaman majalisar na yau Laraba, ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore, bayan da akawun majalisar Alhaji Bashir Idris Ɗiso, ya gabatar da karatun na ɗaya.

Har ila yau, yayin zaman na yau, majalisar ta buƙaci gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ta tallafa wa wasu kanikawa da kafintoci bisa iftila’in gobarar da ta ƙone musu kaya na miliyoyin Naira, tare da asarar rayuka a kan titin Lawan Dambazau.

Majalisar ta buƙaci hakan ne biyo bayan ƙudurin gaggawa da wakilin ƙaramar hukumar Birni da kewaye Alhaji Sarki Aliyu Daneji ya gabatar.

Yayin gabatar da ƙuɗurin, ɗan majalisar ya nemi gwamnatin data tallafa wa waɗanda gobarar ta shafa domin rage musu raɗaɗin iftila’in.

Majalisar ta kuma bukaci gwamnatin da ta ɗaga darajar asibitin garin Gano, zuwa matakin babban asibiti domin ƙara inganta kiwon lafiya a yankin har ma da sauran yankuna, kamar yadda ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Shu’aibu Rabi’u ya buƙata.

Wakilinmu na majalisar Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito cewa, a dai zaman na yau Laraba, shi ma ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ƙaraye, Injiniya Ahmed Ibrahim, ya gabatar da ƙudurin neman gwamnatin Kano ta gina titi a hanyar da ta tashi daga mahaɗar titin zuwa sansanin horas da matasa ƴan hidimar ƙasa, ta bi ta Kurugu da Dederi har zuwa Yammedi duk a yankin ƙaramar hukumar Ƙaraye.

Continue Reading

Labarai

Gwamnan kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sauya shugaban hukumar tattara haraji na jihar

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗin Dakta Zaid Abubakar, a matsayin sabon shugaban hukumar tattara kuɗaɗen haraji ta jihar Kano, da kuma Kasim Ibrahim a matsayin babban daraktan hukumar.

Babban daraktan yaɗa labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar da aka aikowa Dala FM Kano, a daren jiya Laraba.

Sanarwar ta ce, tsohon shugaban hukumar Alhaji Sani Abdulkadir Dambo, an mayar da shi ne a matsayin mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin zuba jari, wanda kuma sauye-sauyen za su fara aiki nan take.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur: Fadar shugaban ƙasa kiyi wani abu dan mutane su samu sauƙi – Ƙungiyar Nothern Concern Soliderity

Published

on

Yayin da al’umma ke ci gaba da fuskantar wahalar man fetur a ƙasar nan, ƙungiyar da ta damu da abubuwan da suka shafi arewacin ƙasar nan ta Northern Concern Soliderity, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi abinda ya dace dan ganin mutane sun samu wani sauƙi.

Babban jami’in gudanarwar ƙungiyar, kuma sakataren riƙo na zauren gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya, Kwamared Saddat Usman Maiyaƙi, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, lokacin da yake nuna takaici kan irin wahalar da al’ummar ƙasa suke sha wajen shan man Fetur a gidajen man.

Ya ce duba da halin matsin rayuwar da al’umma suka samu kansu a ciki, akwai buƙatar shugabanni da masu ruwa da tsaki su kawo ƙarshen wahalar man Fetur ɗin da aka fama da ita.

Kwamared Saddat Maiyaƙi, ya kuma haƙurƙurtar da al’ummar ƙasar nan kan halin ƙuncin rayuwar da suka samu kai a ciki, inda ya yi fatan komai ya zo karshe cikin ƙanƙanen lokaci.

Continue Reading

Trending