Connect with us

Labarai

Mu na neman tallafin gyaran hanya – Dagacin Charo

Published

on

Dagacin garin Charo dake yankin ƙaramar hukumar Gezawa Malam Uzairu Musa Ɗan Kado, ya buƙaci gwamnatin Kano da ta tallafawa yankinsu da gyaran hanyarsu da ta taso daga bakin titi zuwa cikin garin, domin rabuwa da matsalar da suke fuskanta.

Malam Uzairu Ɗan Kado ya buƙaci hakan ne, a yayin taron sada zumunta da Ɗaliban Tsangayar Alaramma Malam Usman mai buya suka shirya, a unguwar Charo dake yankin ƙaramar hukumar Gezawa a ƙarshen makon da ya gabata.

Yana mai cewa, “A lokuta da dama muna fuskantar matsalar rashin hanya, musamman lokutan damuna, wanda mu kan rasa hanyar da za mu bi idan ruwa ya cika hanyar, saboda haka mu ke neman gwamnatin da ta tallafa mana”. A cewar Malam Uzairu.

Da yake nasa jawabin, shugaban taron Malam Usman Ahmad mai buya, miƙa godiyarsa yayi ga waɗanda suka shirya taton, tare kuma da kira ga al’umma da su kara kaimi wajen sada zumunci, domin rabauta da rahmar Allah S.W.T.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Al’umma da dama ne suka samu damar halartar taron, daga sassan jihar Kano, wasu kuma daga jahohin Arewacin Najeriya.

 

Labarai

Mu takaita dogon buri a cikin al’amuran mu – Limamin Tukuntawa

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Jami’urrasul dake unguwar Tukuntawa gidan maza a karamar hukumar Birni, Malam Abubakar Ahmad Sorondinki, ya ja hankalin al’umma da su guji son zuciya da kuma dogon buri a cikin al’amuran abin duniya domin cikin abubuwan da su ke halakar da Dan Adam.

Malam Abubakar Sorondinki, ya yi jan hankalin ne yayin hudubar juma’ar da ya gabatar, a masallacin Juma’a na Jami’urrasul.

Ya ce, “Manzon Allah ya gargadi al’umma da su takaita buri a cikin al’amuran su, saboda haka lallai kullum mu rinka tunanin ajalin mu ya na tare da mu, yin hakan zai kara mana tsoron Allah da kuma nisantar duk abin da zai sabawa Allah”. Inji Malam Abubakar Sorondinki.

Continue Reading

Labarai

Masu siyar da kayan masarufi su ji tsoron Allah kada su kara kudi – Aminu Gyaranya

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Amirul Jaishi, Malam Aminu Abbas Gyaranya, ya ce, al’umma su guji alfasha da rigima a watan auzmin Ramadan domin lokaci ne ibada da zikirai a ko’ina.

Ya ce, “Ana bukatar a yawaita ciyarwa da bayar da taimako, domin manzon Allah (S.W.A) ya na ninka kyautar sa watan Ramadan”.

Malam Aminu Gyaranya, ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa masu sayar da kayan masarufi, da su ji tsoron Allah kada su karawa kaya kudi su saukaka domin Allah zai ba su lada.

Continue Reading

Labarai

Watan Azumi: Mahukunta su nemi hanyar saukaka rayuwar al’umma – Limamin Gwazaye

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Ammar Bin Yasir dake unguwar Gwazaye, Malam Zubair Almuhammady ya yi kira ga mahukunta da su nemo hanyar da za su saukakawa rayuwar al’umma a watan azumin Ramadan.

Almuhammady, ya yi kiran ne a cikin hudubar juma’a da ya gabatar a masallacin na Ammar Bin Yasir.

Ya na mai cewa, “Allah ya jibintawa mahukunta al’amuran al’umma gaba daya, saboda haka akwai bukatar su nemo hanyar da za su saukakawa al’umma domin jin dadin rayuwa a watan azumi”.

Ya kuma ce, “Su sani cewa, kowane shugaba mai kiwo ne kuma Allah zai tambaye shi wannan amanar kiwon da ya ba shi a ranar gobe kiyama, saboda haka al’umma ba za su samu nutsuwa ba har sai sun sami abinci da kuma samar da tsaro a wannan lokaci”. Inji Malam Zubair.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!