Connect with us

Labarai

Idan Kwankwaso na son dawowa APC sai ya yiwa Ganduje biyayya – Aminu Black

Published

on

Dan Jam’iyyar APC a jihar Kano, Aminu Black Gwale, kuma guda daga cikin magoya bayan tsagin Gandujiyya  ya ce, tsarin da ‘yan Jamiyyar PDP kwankwasiyya su ke kai a yanzu ya nuna cewa, ba su shirya karbar mulki ba a hannun APC  a zaben 2023.

Aminu Black ya bayyana hakan ne ta cikin Shirin siyasa Hangen Dala, na gidan rediyon Dala a ranar  Alhamis.

Ya ce, “Mu na sane da yadda Madugun PDP ya ke zuwa wurare daban-daban domin sahale masa ya dawo Jam’iyyar APC, wanda kuma su ke watsa masa kasa a ido”

Ya kuma ce “Matukar kwankwaso na son dawowa cikin APC to babu makawa sai ya risunawa gwamna Ganduje domin shi ne jagoran APC a jihar Kano”. A cewar Aminu Black Gwale.

Kazalika, Aminu Black Gwale ya kuma nuna takaicin sa, kan yadda wasu ke fara hasashen gadon kujerar gwamnan Kano tun yanzu, lamarin da ya ce, babu wani raba gardama a Jam’iyyar APC, kuma a jira zuwa lokacin ya zo tukunna.

Labarai

Mu takaita dogon buri a cikin al’amuran mu – Limamin Tukuntawa

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Jami’urrasul dake unguwar Tukuntawa gidan maza a karamar hukumar Birni, Malam Abubakar Ahmad Sorondinki, ya ja hankalin al’umma da su guji son zuciya da kuma dogon buri a cikin al’amuran abin duniya domin cikin abubuwan da su ke halakar da Dan Adam.

Malam Abubakar Sorondinki, ya yi jan hankalin ne yayin hudubar juma’ar da ya gabatar, a masallacin Juma’a na Jami’urrasul.

Ya ce, “Manzon Allah ya gargadi al’umma da su takaita buri a cikin al’amuran su, saboda haka lallai kullum mu rinka tunanin ajalin mu ya na tare da mu, yin hakan zai kara mana tsoron Allah da kuma nisantar duk abin da zai sabawa Allah”. Inji Malam Abubakar Sorondinki.

Continue Reading

Labarai

Masu siyar da kayan masarufi su ji tsoron Allah kada su kara kudi – Aminu Gyaranya

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Amirul Jaishi, Malam Aminu Abbas Gyaranya, ya ce, al’umma su guji alfasha da rigima a watan auzmin Ramadan domin lokaci ne ibada da zikirai a ko’ina.

Ya ce, “Ana bukatar a yawaita ciyarwa da bayar da taimako, domin manzon Allah (S.W.A) ya na ninka kyautar sa watan Ramadan”.

Malam Aminu Gyaranya, ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa masu sayar da kayan masarufi, da su ji tsoron Allah kada su karawa kaya kudi su saukaka domin Allah zai ba su lada.

Continue Reading

Labarai

Watan Azumi: Mahukunta su nemi hanyar saukaka rayuwar al’umma – Limamin Gwazaye

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Ammar Bin Yasir dake unguwar Gwazaye, Malam Zubair Almuhammady ya yi kira ga mahukunta da su nemo hanyar da za su saukakawa rayuwar al’umma a watan azumin Ramadan.

Almuhammady, ya yi kiran ne a cikin hudubar juma’a da ya gabatar a masallacin na Ammar Bin Yasir.

Ya na mai cewa, “Allah ya jibintawa mahukunta al’amuran al’umma gaba daya, saboda haka akwai bukatar su nemo hanyar da za su saukakawa al’umma domin jin dadin rayuwa a watan azumi”.

Ya kuma ce, “Su sani cewa, kowane shugaba mai kiwo ne kuma Allah zai tambaye shi wannan amanar kiwon da ya ba shi a ranar gobe kiyama, saboda haka al’umma ba za su samu nutsuwa ba har sai sun sami abinci da kuma samar da tsaro a wannan lokaci”. Inji Malam Zubair.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!