Connect with us

Labarai

Iyaye su ƙara mayar da hankali kan karatun ‘ya’yan su – Ibni Sina

Published

on

Babban Kwamandan hukumar hisbah ta jihar Kano Sheikh Harun Muhammad Sani Ibn Sina, ya bukaci iyayen yara da su kara mayar da hankali wajen kulawa da karatun ya’yansu.

Sheikh Harun Ibn Sina ya bayyana hakan ne, ta bakin kwamandan hisbah na karamar hukumar Kumbotso Gwani Murtala Mahmud, wanda ya wakilci babban kwamanda hisbar a yayin saukar karatun Alqur’ani mai girma, da makarantar Naftahurrahman fitta’alim wa kira’atul Qur’an ta gudanar cikin unguwar Sheka Baranda unguwar Fulani dake karamar hukumar kumbotso na dalibai sittin maza goma mata hamsin.

Ya ce, “Kamata ya yi iyaye su fi mayar da hankali ga ilmin addini ga ‘ya’yansu, maimakon fifiko da suke nunawa a bangaren karatun boko”.

Da yake nasa jawabin, shugaban makarantar Gwani Muhammad Muhammad, jan hankalin masu hannu da shuni da kuma gwamnati ya yi, da su kara himma wajen tallafawa makarantar da abinda ya sawwaka, domin kai makarantar ga gaci.

Wakilin Abdulkadir Muhammad Sani Tukuntawa ya rawaito mana cewa, taron ya samu halartar manyan baki daga sassa daban daban, daga ciki kuwa akwai Yariman Kano Alhaji Lamido Abubakar bayero, da kuma shugaban ma’aikata Na yankin karamar hukumar kumbotso Wanda ya wakilici shugaban karamar hukumar kumbotso.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Mu takaita dogon buri a cikin al’amuran mu – Limamin Tukuntawa

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Jami’urrasul dake unguwar Tukuntawa gidan maza a karamar hukumar Birni, Malam Abubakar Ahmad Sorondinki, ya ja hankalin al’umma da su guji son zuciya da kuma dogon buri a cikin al’amuran abin duniya domin cikin abubuwan da su ke halakar da Dan Adam.

Malam Abubakar Sorondinki, ya yi jan hankalin ne yayin hudubar juma’ar da ya gabatar, a masallacin Juma’a na Jami’urrasul.

Ya ce, “Manzon Allah ya gargadi al’umma da su takaita buri a cikin al’amuran su, saboda haka lallai kullum mu rinka tunanin ajalin mu ya na tare da mu, yin hakan zai kara mana tsoron Allah da kuma nisantar duk abin da zai sabawa Allah”. Inji Malam Abubakar Sorondinki.

Continue Reading

Labarai

Masu siyar da kayan masarufi su ji tsoron Allah kada su kara kudi – Aminu Gyaranya

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Amirul Jaishi, Malam Aminu Abbas Gyaranya, ya ce, al’umma su guji alfasha da rigima a watan auzmin Ramadan domin lokaci ne ibada da zikirai a ko’ina.

Ya ce, “Ana bukatar a yawaita ciyarwa da bayar da taimako, domin manzon Allah (S.W.A) ya na ninka kyautar sa watan Ramadan”.

Malam Aminu Gyaranya, ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa masu sayar da kayan masarufi, da su ji tsoron Allah kada su karawa kaya kudi su saukaka domin Allah zai ba su lada.

Continue Reading

Labarai

Watan Azumi: Mahukunta su nemi hanyar saukaka rayuwar al’umma – Limamin Gwazaye

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Ammar Bin Yasir dake unguwar Gwazaye, Malam Zubair Almuhammady ya yi kira ga mahukunta da su nemo hanyar da za su saukakawa rayuwar al’umma a watan azumin Ramadan.

Almuhammady, ya yi kiran ne a cikin hudubar juma’a da ya gabatar a masallacin na Ammar Bin Yasir.

Ya na mai cewa, “Allah ya jibintawa mahukunta al’amuran al’umma gaba daya, saboda haka akwai bukatar su nemo hanyar da za su saukakawa al’umma domin jin dadin rayuwa a watan azumi”.

Ya kuma ce, “Su sani cewa, kowane shugaba mai kiwo ne kuma Allah zai tambaye shi wannan amanar kiwon da ya ba shi a ranar gobe kiyama, saboda haka al’umma ba za su samu nutsuwa ba har sai sun sami abinci da kuma samar da tsaro a wannan lokaci”. Inji Malam Zubair.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!