Connect with us

Labarai

Yadda ma’aikatan shari’a su ka gudanar da yajin aiki

Published

on

Kungiyar ma’aikatan shari’a ta kasa reshen jihar Kano ta ce, sun shiga yajin aiki ne saboda rashin samun Hakkin yancin gashin kan su a jihar.

Sakataren kungiyar ma’aikatan shari’ar, Kwamared Sulaiman Aliyu ya bayyana hakan a shelkwatar babbar kotun jihar Kano dake Audo Bako yayin da take a garkame sakamakon yajin aikin da su ka fara tun a daren Laraba.gudanarwa.

Ya ce, “Mun samu umarnin ne daga uwar daga uwar kungiya ta kasa kan tsunduma yajin aikin, wanda sashe na 121 ya tabbatar mana da wannan ‘yanci, amma an kasa ba mu”.

Ya kuma ce, “hukumomi su ne ya kamata su yi abinda ya dace, saboda halin da al’umma za su shiga ba za mu dauke kai ga hakkokin ma’aikatan shari’a ba, domin suma al’umma za su amfana da al’amarin wajen samun daidaito da adalci a shari’a”. A cewar Kwamared Sulaiman.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewar, wani lauya mai suna barista Ahmad A Gwadabe ya bayyana cewar, babu dadi ma’aikatan su yi yajin aiki domin abubuwa da yawa za su tsaya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Mu takaita dogon buri a cikin al’amuran mu – Limamin Tukuntawa

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Jami’urrasul dake unguwar Tukuntawa gidan maza a karamar hukumar Birni, Malam Abubakar Ahmad Sorondinki, ya ja hankalin al’umma da su guji son zuciya da kuma dogon buri a cikin al’amuran abin duniya domin cikin abubuwan da su ke halakar da Dan Adam.

Malam Abubakar Sorondinki, ya yi jan hankalin ne yayin hudubar juma’ar da ya gabatar, a masallacin Juma’a na Jami’urrasul.

Ya ce, “Manzon Allah ya gargadi al’umma da su takaita buri a cikin al’amuran su, saboda haka lallai kullum mu rinka tunanin ajalin mu ya na tare da mu, yin hakan zai kara mana tsoron Allah da kuma nisantar duk abin da zai sabawa Allah”. Inji Malam Abubakar Sorondinki.

Continue Reading

Labarai

Masu siyar da kayan masarufi su ji tsoron Allah kada su kara kudi – Aminu Gyaranya

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Amirul Jaishi, Malam Aminu Abbas Gyaranya, ya ce, al’umma su guji alfasha da rigima a watan auzmin Ramadan domin lokaci ne ibada da zikirai a ko’ina.

Ya ce, “Ana bukatar a yawaita ciyarwa da bayar da taimako, domin manzon Allah (S.W.A) ya na ninka kyautar sa watan Ramadan”.

Malam Aminu Gyaranya, ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa masu sayar da kayan masarufi, da su ji tsoron Allah kada su karawa kaya kudi su saukaka domin Allah zai ba su lada.

Continue Reading

Labarai

Watan Azumi: Mahukunta su nemi hanyar saukaka rayuwar al’umma – Limamin Gwazaye

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Ammar Bin Yasir dake unguwar Gwazaye, Malam Zubair Almuhammady ya yi kira ga mahukunta da su nemo hanyar da za su saukakawa rayuwar al’umma a watan azumin Ramadan.

Almuhammady, ya yi kiran ne a cikin hudubar juma’a da ya gabatar a masallacin na Ammar Bin Yasir.

Ya na mai cewa, “Allah ya jibintawa mahukunta al’amuran al’umma gaba daya, saboda haka akwai bukatar su nemo hanyar da za su saukakawa al’umma domin jin dadin rayuwa a watan azumi”.

Ya kuma ce, “Su sani cewa, kowane shugaba mai kiwo ne kuma Allah zai tambaye shi wannan amanar kiwon da ya ba shi a ranar gobe kiyama, saboda haka al’umma ba za su samu nutsuwa ba har sai sun sami abinci da kuma samar da tsaro a wannan lokaci”. Inji Malam Zubair.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!