Connect with us

Labarai

Mu na samun nasarar dakile laifuka da taimakon al’umma – DSP Kiyawa

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta ja hankalin al’umma da su ci gaba da sanar da jami’an tsaro bayanan sirri kan wani motsi da su kaga ana yi a cikin unguwa wanda ba su yarda da shi ba.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Dansanda da Jama’a na gidan rediyon Dala, wanda ke zuwa a duk ranar Talata.

Ya ce, “Aikin samar da tsaro a jihar Kano ba na rundunar ‘yan sanda ba ne kadai, akwai bukatar al’umma su bada gudunmawa, wajen bayar da bayanan wasu abubuwa da ake yi a unguwanni na laifuka”.

Ya kuma ce, “Bayanan da al’umma ke ba su, ya sa su ka samu nasarar kama wani mutum da ake zargin sa ya na garkuwa da fashin Shanu, kuma aka wakilta shi domin kafa sansanin boye wadanda su ka yi garkuwa da su a jihar Kano, sannan kuma su ka samu nasarar kama wani mutum dake sarrafa kaya na jabu a gidansa dake unguwar Sabon Gari”. A cewar DSP Abdullahi Kiyawa.

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya kuma tabbatar da cewar, duk wanda ya ba su wani bayanan sirri a kan wani laifi da ake aikatawa za su yi kokarin boye sirrin sa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Mu takaita dogon buri a cikin al’amuran mu – Limamin Tukuntawa

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Jami’urrasul dake unguwar Tukuntawa gidan maza a karamar hukumar Birni, Malam Abubakar Ahmad Sorondinki, ya ja hankalin al’umma da su guji son zuciya da kuma dogon buri a cikin al’amuran abin duniya domin cikin abubuwan da su ke halakar da Dan Adam.

Malam Abubakar Sorondinki, ya yi jan hankalin ne yayin hudubar juma’ar da ya gabatar, a masallacin Juma’a na Jami’urrasul.

Ya ce, “Manzon Allah ya gargadi al’umma da su takaita buri a cikin al’amuran su, saboda haka lallai kullum mu rinka tunanin ajalin mu ya na tare da mu, yin hakan zai kara mana tsoron Allah da kuma nisantar duk abin da zai sabawa Allah”. Inji Malam Abubakar Sorondinki.

Continue Reading

Labarai

Masu siyar da kayan masarufi su ji tsoron Allah kada su kara kudi – Aminu Gyaranya

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Amirul Jaishi, Malam Aminu Abbas Gyaranya, ya ce, al’umma su guji alfasha da rigima a watan auzmin Ramadan domin lokaci ne ibada da zikirai a ko’ina.

Ya ce, “Ana bukatar a yawaita ciyarwa da bayar da taimako, domin manzon Allah (S.W.A) ya na ninka kyautar sa watan Ramadan”.

Malam Aminu Gyaranya, ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa masu sayar da kayan masarufi, da su ji tsoron Allah kada su karawa kaya kudi su saukaka domin Allah zai ba su lada.

Continue Reading

Labarai

Watan Azumi: Mahukunta su nemi hanyar saukaka rayuwar al’umma – Limamin Gwazaye

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Ammar Bin Yasir dake unguwar Gwazaye, Malam Zubair Almuhammady ya yi kira ga mahukunta da su nemo hanyar da za su saukakawa rayuwar al’umma a watan azumin Ramadan.

Almuhammady, ya yi kiran ne a cikin hudubar juma’a da ya gabatar a masallacin na Ammar Bin Yasir.

Ya na mai cewa, “Allah ya jibintawa mahukunta al’amuran al’umma gaba daya, saboda haka akwai bukatar su nemo hanyar da za su saukakawa al’umma domin jin dadin rayuwa a watan azumi”.

Ya kuma ce, “Su sani cewa, kowane shugaba mai kiwo ne kuma Allah zai tambaye shi wannan amanar kiwon da ya ba shi a ranar gobe kiyama, saboda haka al’umma ba za su samu nutsuwa ba har sai sun sami abinci da kuma samar da tsaro a wannan lokaci”. Inji Malam Zubair.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!