Connect with us

Labarai

Wadda aka yiwa aikin Tiyata kada ta bari ta haihu a gida – Dakta Magashi

Published

on

Ƙwararren likitan mata dake asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, Dakta Mahmud Kawu Magashi, ya ce, duk macen da a ka yi wa aiki na (CS) a yayin haihuwa, kar ta sake ta ƙara yadda ta haihu da kan ta a gida, domin gudun fuskantar matsala da za ta iya haihafar da gagrumar matsala.

Dakta Mahmud Kawu Magashi, ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Mu Tambayi Likita na gidan rediyon Dala FM, wanda ya gudana da a ranar Talata da ƙarfe huɗu zuwa biyar.

Yana mai cewa, “Matuƙar mata su ka ce, za su haihu a gida bayan kuma sun san an taba yi musu aiki, za su iya samun matsala”. Inji Dakta Kawu

Dakta Kawu, ya kuma gargaɗi mata masu karɓar haihuwa, dama sauran matan da suke gangancin hawa kan cikin macen da tazo haihuwa domin mace ta yi saurin haihuwa su dai na yin hakan, domin yakan haifar da matsala ga matan.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Dakta Kawu Magashi ya kuma shawarci matan, da su kaucewa barin ana hawar musu kan ciki a yayin da su ka zo haihuwa domin su haihu da wuri, hakan zai haifar musu da matsala.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Mu takaita dogon buri a cikin al’amuran mu – Limamin Tukuntawa

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Jami’urrasul dake unguwar Tukuntawa gidan maza a karamar hukumar Birni, Malam Abubakar Ahmad Sorondinki, ya ja hankalin al’umma da su guji son zuciya da kuma dogon buri a cikin al’amuran abin duniya domin cikin abubuwan da su ke halakar da Dan Adam.

Malam Abubakar Sorondinki, ya yi jan hankalin ne yayin hudubar juma’ar da ya gabatar, a masallacin Juma’a na Jami’urrasul.

Ya ce, “Manzon Allah ya gargadi al’umma da su takaita buri a cikin al’amuran su, saboda haka lallai kullum mu rinka tunanin ajalin mu ya na tare da mu, yin hakan zai kara mana tsoron Allah da kuma nisantar duk abin da zai sabawa Allah”. Inji Malam Abubakar Sorondinki.

Continue Reading

Labarai

Masu siyar da kayan masarufi su ji tsoron Allah kada su kara kudi – Aminu Gyaranya

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Amirul Jaishi, Malam Aminu Abbas Gyaranya, ya ce, al’umma su guji alfasha da rigima a watan auzmin Ramadan domin lokaci ne ibada da zikirai a ko’ina.

Ya ce, “Ana bukatar a yawaita ciyarwa da bayar da taimako, domin manzon Allah (S.W.A) ya na ninka kyautar sa watan Ramadan”.

Malam Aminu Gyaranya, ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa masu sayar da kayan masarufi, da su ji tsoron Allah kada su karawa kaya kudi su saukaka domin Allah zai ba su lada.

Continue Reading

Labarai

Watan Azumi: Mahukunta su nemi hanyar saukaka rayuwar al’umma – Limamin Gwazaye

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Ammar Bin Yasir dake unguwar Gwazaye, Malam Zubair Almuhammady ya yi kira ga mahukunta da su nemo hanyar da za su saukakawa rayuwar al’umma a watan azumin Ramadan.

Almuhammady, ya yi kiran ne a cikin hudubar juma’a da ya gabatar a masallacin na Ammar Bin Yasir.

Ya na mai cewa, “Allah ya jibintawa mahukunta al’amuran al’umma gaba daya, saboda haka akwai bukatar su nemo hanyar da za su saukakawa al’umma domin jin dadin rayuwa a watan azumi”.

Ya kuma ce, “Su sani cewa, kowane shugaba mai kiwo ne kuma Allah zai tambaye shi wannan amanar kiwon da ya ba shi a ranar gobe kiyama, saboda haka al’umma ba za su samu nutsuwa ba har sai sun sami abinci da kuma samar da tsaro a wannan lokaci”. Inji Malam Zubair.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!