Connect with us

Labarai

KEDCO: An yanke mana wuta bayan an karɓi kuɗaɗen mu – Al’ummar Salanta

Published

on

Al’ummar unguwar Sharaɗa Salanta dake yankin ƙaramar hukumar Birni, sun koka kan yadda ma’aikatan wutar lantarki KEDCO, su ka yanke musu wayoyin wuta, yayin da su ka je karɓar kuɗaɗe a wajen su, wanda har yanzu ba su dawo musu da wayoyin ba.

Mutanen sun ce, ma’aikatan wutar sun karɓarwa wasun su, Naira dubu uku, yayin da wata aka karɓar mata Naira dubu biyu da dari biyar, wani kuma naira dubu ɗaya.

Sai dai ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Global Cummunity for Humman Right Network, ƙarƙashin jagorancin Ƙaribu Yahya Lawan Kabara ta ce, za su yi duk mai yiyuwa wajen ganin sun ƙwato musu haƙƙinsu, musamman ma na kuɗaɗen da sukace an karɓar musu, kasancewar mutanen sun kai kokensu ga ƙungiyar.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, mai magana da yawun kamfanin wutar lantarkin a jihar Kano Ibrahim Sani Shawai ya ce, kamfanin ne ya tura ma’aikatan sa domin su je karɓo kuɗaɗen wutar, sai dai koda aka yi masa tambaya akan kuɗaɗen da ma’aikatan na su suka karɓa a wajen mutanen bai ce komai ba, amma za mu ci gaba da bibiya domin sanin matsayin kuɗaɗen waɗanda aka karɓarwa.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending