Connect with us

Labarai

Watan Ramadan: Tallafawa marayu zai rage musu raɗaɗi – Dagacin Gandun Albasa

Published

on

Dagacin Gandun Albasa Injiniya Alƙasim Yakubu, ya shawarci ƙungiyoyi masu zaman kansu, dama sauran al’umma baki ɗaya, da su ƙara ƙaimi wajen tallafawa marasa ƙarfi.

Injiniya Alƙasim Yakubu ya bayyana hakan ne, yayin bayar da tallafin kayan abinci ga iyayen marayu da  gidanauniyar Garu Hira Foundation ta yi, a cikin masallacin Juma’a dake unguwar Tukuntawa dake yankin ƙaramar hukumar Birni a ranar Asabar.

Ya ce, “Matuƙar ƙungiyoyi masu zaman kan su da masu hannu da shuni za su ƙara ruɓanya taimakon masu karamin ƙarfin musamman ma mata da mazajensu su ka rasu, za’a rage musu wani raɗaɗi da yake damun su na rashin mazajen su da su ka yi”. A cewar Injiniya Alƙasim Yakubu.

Da yake nasa jawabin shugaban gidauniyar bayar da tallafin, Malam Adamu Musa Ɗan Azumi, ya bayyana cewar, “Mu na bayar da tallafin ne ga iyayen marayu, dama masu rangwamen gata, domin rage musu wata damuwa da take damun su, kuma mun shirya tsaf domin ci gaba da tallafawa masu buƙata ta musamman a yankin unguwar Tukuntawa dama wasu sassan jihar Kano baki ɗaya”.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, an raba tallafin kayan abincin ga mata kimanin ɗari da goma sha bakwai, wanda mata daga sassa daban-daban su ka zo domin karɓa.

Ilimi

Kai ziyara a ranar Sallar Idi na da muhimmanci a tsakanin al’umma – Limami

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Alaramma Abubakar Ɗan Tsakuwa Mallam Abdulkareem Aliyu ya ce, kai ziyara ga gidajen ‘yan uwa a ranar Sallar Idi abu ne mai matuƙar mahimmanci a rayuwa.

Mallam Abdulkareem ya bayyana hakan ne ta cikin huɗubar Sallar Idi da ya gabatar yau Alhamis a masallacin ga al’ummar Musulmai.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u da ya halarci masallacin ya rawaito cewar, Mallam Abdulkareem Aliyu ya kumace, kamata yayi a irin wannan ranaku Musulmai su rinƙa kai ziyarar musamman ma ga gidajen marayu, gakiyayyu, maƙabartu, da gidan masu rangwamin hankali, inda yace kai ziyarar kansa a samu gwaggwaɓan lada ba ka ɗan ba.

Sannan kuma Malamin ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa da yin addu’a domin neman falalar Allah S.W.T

Continue Reading

Labarai

Huɗubar Sallar Idi: Mu rinƙa taimakawa marayu: Muhammadu Sunusi II

Published

on

Tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi Na biyu, ya ja hankalin al’ummar musulmai da su ƙara mayar da hankali wajen neman ilmin addinin dana zamani, domin  sanin yadda zasu bautawa Allah S.W.T

Muhammadu Sunusi Na biyu ya bayyana hakan ne, a yayin gabatar da huɗubar Sallar Idi da ya gabatar a ranar  Alhamis a Filin Idi na Murtala Muhammad Square dake jihar Kaduna.

Ya kuma yi kira ga al’umma dasu ƙara himma wajen taimakawa marayu tare kuma da sada zumunci a tsakani, domin rabauta da rahamar Allah S.W.T

Wakilin mu Abba Ibrahim Lafazi da ya halarci masallacin a jihar Kadunan, ya rawaito mana cewar, Mallam Muhamadu Sunusi na biyun ya kuma shawarci mutane, da su kaucewa saɓawa Allah S.W.T domin gujewa fushinsa.

Continue Reading

Labarai

Bikin Sallah:  Duk budurwar da ta yi kwalliyar abaya ba ma so a kai kasuwa – Samari

Published

on

Yayin da ake shirye-shiryen bikin Sallah karama, samari sun ce duk budurwar da ta yi kwalliyar abaya ba su a ciki a kai kasuwa.

Sai dai kuma a hannu guda wasu samarin kuwa cewa su ka yi, duk wacce ta yi kwalliyar abayar mai son kudi ce.

Shi kuwa wani matashi ya bayyana ra’ayin sa ne da cewa, duk wanda baya son mai abayar tsoho ne, saboda haka shi mai abayar ma yafi kauna, saboda ita ce wayayya ‘yar zamani, kuma shi yaro ai da yarinya aka san shi.

Haka zalika, wasu matasan a nasu ra’ayin cewa su ka yi, kwata-kwata ma su ba zu su yi budurwar a lokacin wankan sallar ba, saboda gudun kar su dauki Kucaka.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!