Connect with us

Labarai

Iyaye ku ƙara kulawa da karatun ƴaƴan ku – Injiya Hamisu Cidari

Published

on

Shugaban majalisar dokokin jihar Kano Injiniya Hamisu Ibrahim Cidari, ya shawarci iyaye da su ƙara kulawa da karatun ƴaƴansu, domin zama ababen koyi a nan duniya dama ranar gobe ƙiyama.

Hamisu Ibrahim Cidari ya bayyana hakan ne, a yayin saukar Karatun Alkur’ani mai girma, da makarantar Ma’ahad Ɗariƙar Huda ta gudanar cikin unguwar Tudun Wada dake yankin ƙaramar hukumar Ɗan Batta.

Ya ce, “Kamata ya yi iyaye su ƙara ƙaimi wajen sauke nauye-nauyen da Allah (S.W.T) ya ɗora musu na ƴaƴansu”. Inji Injiniya Hamisu Ibrahim Cidari.

Da yake nasa jawabin, Sakataren makarantar Malam Abubakar Kaɗa Bature, kira yayi ga gwamnati da masu hannu da shuni, da su shigo wajen tallafawa makarantun Islamiyya da abubuwan da suka sawwaƙa, domin samar da ci gaban da ya dace.

Wakiliyar mu Khadijah Ishak Muhammad ta rawaito cewa, kimanin ɗalibai 38 ne su ka yi saukar Alƙur’anin mai girma, daga ciki kuwa akwai masu hadda mutane biyar.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending