Labarai
Masu mayukan shafawa sun mika kayyakin da su ka lalace wajen CPC
Kungiyar ma su sayar da mayukan shafawa da dangogin su dake kasuwar, Muhammadu Abubakar Rimi Sabon Gari ta mika gurbatattun mayukan shafawa ga hukumar kare hakkin mai saye da mai sayarwa ta jihar Kano (Consumer Protection Council).
Sanarwar mai kunshe da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar ta KSCPC, Musbahu Aminu Yakasai.
Da ya ke mika kayan ga shugaban hukumar, Dr Baffa Babba Dan Agundi, shugaban kungiyar Alhaji Shu’aibu Salisu, ya ce”Kayan wadanda kudin su ya kai kimanin Naira miliyan biyar, sun hada da man shafawa da man gashi da turare da hoda da kuma sauran nau’ikan kayan kwalliya na mata. Mun samu nasarar kama kayan ne a shaguna daban-daban a cikin kasuwar Sabongari. Daga cikin kayan akwai wanda wa’adin amfanin su ya kare da kuma wanda suka lalace da ma wanda basu da lambar NAFDAC. Kuma za mu cigaba da baiwa hukumar hadin kai wajen yunkurin hana sayarwa ga al’umma kayayyakin da za su iya yin illa ga lafiyar su”.
A nasa jawabin shugaban hukumar kare hakkin mai saye da mai sayarwa ta jihar, Kano Dr. Baffa Babba Dan Agundi ya ce,”Na ji dadin wannan namijin kokari da kungiyar ku ta yi, kuma ku kasance ma su jajircewa wajen bin gaskiya a kasuwancin ku, da kaucewa dabi’ar nan ta sayarwa da mutane kaya marasa kyau. Kuma hukumar mu za ta ci gaba da aiki tare da yin aiki ka’in da na’in, domin samun nasara a wannan bangaren”.
Labarai
Mahukunta ku kawo mana ɗauki a masallacin garin mu – Mazauna garin Ɗan-Dalama
Al’ummar garin Ɗan-Dalama da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, sun koka tare da neman ɗaukin mahukunta kan yadda katangar masallacin Juma’a na garin ta lalace, lamarin da hakan ke barazanar faɗuwar katangar.
Shugaban kwamitin masallacin juma’ar na garin Ɗan Dalama, Mallam Muhammad Mai Nama, ne ya magantu kan al’amarin, inda ya kuma yi kira ga al’umma ciki har da Attajirin ɗan kasuwar nan Alhaji Alhassan Aminu Ɗan Tata, da su kawo musu ɗauki domin gyara katangar masallacin na Ɗan Dalama, bisa yadda take neman faɗuwa.
Ya kuma ƙara da cewa ba iya katangar ce ke barazanar faɗuwar ba, haka ma cikin masallacin ba a cewa komai, duk kuwa da ƴan kwamitin sun yi bakin ƙokarin su, amma dai kawo yanzu akwai gyare-gyaren da ya ke buƙata.
Labarai
Ba za’a iya wadata mutane da Fetur ba idan gwamnati ba ta sa hannu ba – Bashir Ɗan Mallam
Yayin da ake ci gaba da fuskantar tsadar man fetur a ƙasar nan, shugaban kungiyar Dillalan Man fetur da Iskar Gas, ta ƙasa Bashir Ahmad Ɗan malam, ya ce koda kuwa matatar Mai ta Dangote za ta yi ƙarfi ka’in da na’in, ba lallai ne a samu saukin Man fetur ba a ƙasa, matuƙar gwamnatin tarayya bata sa hannu ba.
Bashir Ɗan Malam ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da gidan rediyon Dala FM, da safiyar yau Juma’ar.
Ɗan Mallam ya kuma ce sakamakon yadda gwamnati take taimakawa a fagen shan man, hakan yasa idan har bata sanya hannu ba za’a rinƙa shan wahala wajen samun man fetur ɗin a ƙasa.
Wannan dai na zuwa ne yayin da al’umma ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsadar man fetur, lamarin da ya sa ake siyar da kowacce lita sama da Naira 800 a jihar Kano, inda ake ci gaba da fuskantar manyan layuka a gidajen man da dama.
Labarai
Zamu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ƴan Jarida – Hukumar Zaɓe ta Kano
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSEC, ta sha alwashin aiki kafaɗa-kafaɗa da ma’aikatan Jarida, musamman ma da zaɓen ƙananan hukumomin jihar nan 44 da ke tafe.
Sabon shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan Manumfashi, ne ya bayyana hakan, yayin ziyarar da tawagar ƙuniyar matasan ƴan Jarida, ta Kano Youth Journalist Forum, suka kai masa a ofishin sa yau Alhamis, yayin da ya shafe kwanaki huɗu da kama aiki.
Ya kuma ce, za su yi aiki da ma’aikatan Jarida musamman ma yayin gudanar da ayyukan zaɓen ƙananan hukumomin Kano 44, da ke tafe, domin wayar da kan al’umma da ma samun nasara yayin zaɓen da ma bayan sa.
Farfesa Manumfashi, ya kuma ƙar da cewa, akwai buƙatar kowa ya bayar da tasa gudummawar a harkar zaɓe, domin kuwa yanzu haka suna ci gaba da aiki wajen shirya zaɓen ƙananan hukumomin.
Da yake nasa jawabin shugaban ƙungiyar matasa ƴan Jaridar ta jihar Kano Musa Zangina Adam, ya ce sun kai ziyarar ne, domin su ƙulla alaƙar aiki a tsakanin su da hukumar, bisa yadda kowanne ɓangare yake buƙatar juna, tare kuma da bayar da gudunmawar da ya kamata.
Zangina, ya kuma ce a shirye ƙungiyar su take wajen ci gaba da bibiyar al’amuran da suka shafi al’umma, tare da nusar da mahukunta dan ganin an wadata su da kayayyakin more rayuwa.
-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su