Connect with us

Lafiya

Mai Kalwa: A na zargin wata mata da satar Akuya

Published

on

Mai Unguwar Mai Kalwa dake yankin karamar hukumar Kumbotso, Malam Basiru Dahiru Yakubu, wanda a ka fi sani da mai unguwa na Amira ya ce ya yi matukar mamakin yadda a ka kama wata tsohuwar mata da zargin satar AKuya a unguwar ta Mai Kalwa.

Malam Basiru Dahiru Yakubu ya bayyana hakanne aganawarsa da gidan rediyon Dala a yayin da a ka kama matar da a ke zargin.

Malam Basiru Dahiru Yakubu ya kuma kara da cewar,”Bayan bincike da na yi na gano wacce a ke zargi da satar Akuyar dama halin ta ne, ba za mu zuba ido mu ga a na shigowa yankin a na yin irin wannan hali na satar dabbobi ba, kuma al ummar mai kalwa sun yi kokari kan yadda ba su dauki doka a hannu ba”.

Sha’aibu Hassan Sa’id daya ne daga cikin matasan da suka kama matar ya kuma kara da cewa,”Ina kwance a daki a ka ce min ga wata mata ta saci akuya, amma koda na fito ban gantaba ba sai yaron da tasa ya kama mata akuyar, amma daga bisani na bincikota ta buya a wani gida kamar yadda yaron gidan ya sheda min”.      

Malam Yusif Shehu shi ne wanda a ka sace wa Akuyar ya ce,”Dama an dade a na sace mana Tumaki da Akuyoyi tun a baya, amma gashi Allah ya toni asirin mai satar, yara su guji aiwatar da aiki ga wani bako da basu san shi ba”.

Wakilinmu Nasir Khalid Abubakr ya rawaito cewa tuni a ka mika matar ga hukumar ‘yansandan Naibawa, domin gudanar da bincike a kan ta.

Labarai

Jinya da Ungozoma: Duk ma’aikacin da ya karya doka za a dauki mataki

Published

on

Mataimakin shugaban kungiyar ma’aikatan Jinya da Ungozoma na kasa, Kwamared Musa Ibrahim Amadu, ya ja hankalin ma’aikatan Jinya, da su kara kulawa da ayyukan su na yau da kullum, domin kaucewa fadawa cikin matsala.

Kwamared Musa Ibrahim, ya bayyana hakan ne a ya yin taron bankwana da shugaban Asibitin kashi na Dala Dr. Muhammad Nuhu Salihu, bisa samun sauyin wajen aiki da ya yi, wanda zai kammala aiki a Asibitin nan da mako guda mai zuwa.

Ya ce,”Matukar a ka samu ma’aikatan Jinya da Ungozoma da karya doka a yayin gudanar da ayyukan su, to kuwa shakka babu za a dauki mataki a kan su, kamar yadda a ka samar da dokar hakan”. Inji Kwamrade Musa.

Da ta ke na ta jawabin, shugabar kungiyar Unguzoma ta jihar Kano, Hajiya Nafisa Talatu Musa, Maman Alheri cewa ta yi,”Mun shirya taron ne domin yin bankwana tare kuma da karrama Dr Muhammad Nuhu, bisa yadda ya bayar da gudunmawarsa ga al’umma a yayin gudanar da aikin sa”.

Sai dai shugaban Asibitin kashi na Dala Dr Muhammad Salihu ya ce,“Na yi matukar farin ciki bisa yadda dukkanin ma’aikatan Asibitin dama sauran ‘yan uwa da abokanan arziki su ka nuna min kauna, kuma ma’aika mu kara dagewa a a kan ayyukan mu na yau da kullum”. Inji Dr Salihu.

Wakilan mu da suka halarci wajen taron, Hassan Mamuda Ya’u da Maryam Muhammad Usman, sun rawaito mana cewa, shugaban Asibitin mai barin gado Dr Salihu, ya kuma shawarci ma’aikatan Asibitin da su kasance masu biyayya ga sabon shugaban da za a kawo musu nan gaba.

Continue Reading

Lafiya

Ana zargin namiji da afkawa wani yaro

Published

on

Babbar kotun shari’ar Musulunci dake zamanta a Kafin Mai Yaƙi a ƙaramar hukumar Kiru, ƙarƙashin mai Shari’a Ustaz Sani Salihu, ta ci gaba da sauraron shari’ar wani magidanci mazaunin garin Yako mai kimanin sama da shekaru Hamsin, da ake zarginsa da haikewa wani ƙaramin yaro ɗan kimanin shekaru Takwas.

A zaman  na ranar Litinin, ko da Ɗan Sanda mai gabatar da ƙara Sajan Aminu Ƙofar Wambai, wanda ya fito daga sashin binciken manyan laifuka dake unguwar Bompai, ya roƙi kotun, da ta bayar da izini a mayar da magidancin sashin binciken manyan laifuka, domin faɗaɗa bincike, dogaro da sashi na 298, wato Further Investigation, a nan ne Alƙalin kotun Shehun Malami Sani Salihu ya ce, Kotun za ta yi nazari kan roƙon da Sajan Aminu Ƙofar Wanbam ya yi.

Kotun ta bayar da umarnin ci gaba da tsare magidancin a gidan ajiya da gyaran hali, zuwa lokacin da ta yi nazari kan roƙon.

Bayan da aka fito daga kotun ne kuma, mu ka ji ta bakin mahaifin yaron wanda ya nemi kotun da ta nema musu haƙƙin ɗansu, domin kuwa har sau biyar yana amfani da yaron namu.

Shima kuma magidancin da ake zargi da nuna halin ta idon, ya ce, “Zargin da ake mini ba gaskiya ba ne ba, ko Alƙur’ani aka bani zan iya rantsewa akan zargin da ake mini, koda kuwa zan mutum bayan na rantse, domin ban ma san yaron da aka alaƙantani dashi ba” Inji Auwalu Coach.

 

Continue Reading

Labarai

Gurbataccen Abinci: Mun kama Dusar Dabbobi a Kano – CPC

Published

on

Hukumar kare hakkin mai siye da siyarwa Consumer Protection Council (CPC) ta kama wata Dusar Dabbobi wanda a ka gurbata ta da Buntun Shinkafa.

Hukumar ta dai kai sumamen ne a kasuwar Singa dake jihar Kano.

Babban mataimaki na musamman ga gwamna a hukumar KAROTA, Nasiru Usman Na’ibawa ya ce”Mun samu rahoton gurbatacciyar Dusar ne daga wani mutum da ya saya a kasuwar Singa, ita kuma hukuma ta bincika ta kuma tabbatar da rashin ingancin Dusar ta je ta kama

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!