Connect with us

Labarai

Kotu ta bayar da umarnin datse hannun wani matashi

Published

on

Babbar kotun shari’ar musulinci dake Shahuci karkashin mai shari’a Salisu Umar Abdullahi ta yankewa wani matashi hukuncin yanke hannu a mayar da shi Dungulmi, sannan kuma ya yi  rantsuwa da Alkur’ani mai girma.

Tun da fari an yi zargin matashin fasa wani shago a kasuwar Kurmi, sai dai mai gadin shagon ya tare shi amma ya ki tsayawa, da yake kakkarfa ne ya kutsa kai cikin shiga shagon ya dauki Injin ban ruwa da Injin bayar da hasken wutar lantarki wato (Generator) da kofa waya, dama wasu kayan da akai musu kimar kudi naira dubu sittin, sai kuma ruwan kudi naira dubu ashirin da bakwai.

Matashin ya amsa ya dauki kayayyakin ya kuma musa kudaden, ita kuma kotun ta yi umarnin a datse masa hannun dama ya koma Dungulmi, akan laifin da ya amsa, kamar yadda sashi na 134 na kundin shari’ar musulinci na shekarar 2000 ya tanada, tunda dai abun da ya sata din ya kai daya bisa hudun dinare naira dubu 22.

Kotun ta yi umarnin a bashi Alkurani mai girma ya ranste da shi, kamar yadda lauyan gwamnati dake gabatar da kara a kotun Zaharraddin Mustafa ya yi mana karin haske.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending