Connect with us

Labarai

A dakile illlar da wata tsutsa ke yi a gonakin yankin Doguwa – Majalisar Dokoki

Published

on

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi Kira ga gwamnatin Jihar da ta hanzarta Kai dauki ga manoma a Kananan Hukumomin Doguwa da Tudun Wada domin dakile illar da wata tsutsa ke yi a gonakin manoma a wadancan yankuna.

A cikin kudurin gaggawa da Dan Majalisa Mai Wakiltar Karamar Hukumar Doguwa Hon Salisu Muhammad Ibrahim ya gabatar a Zauren Majalisar a zamanta na ranar Litinin.

Ya ce, “Irin wadannan tsutsotsi su na barazana tare da karya manoma a gonakin su domin duk gonar da suka shiga to sai sun cinye shukar da aka yi tas cikin dan kankanen lokaci”.

Ya kuma ce, “Rashin samun dauki a cikin dan kankanen lokaci daga gwamnatin jiha na iya jefa manoman cikin mummunan hali, wanda hakan ka iya shafar noman abinci na bana idan aka yi la’akari da Karamar Hukumar Doguwa yankin ne  wanda ke samar da mafi yawancin  abincin da ake samu a Jihar nan”. Inji Hon Salisu Muhammad.

Kudurin ya sami goyon bayan ‘Yan Majalisu masu Wakiltar Kananan Hukumomin Tudun Wada da kuma na Kiru inda dukkansu su ka tabbatarwa Zauren Majalisar cewar su na da labarin bullar wannan tsutsa da kuma irin illar da ta keyi a gonakin manoma tare da neman Majalisar ta yi Kira na gaggawa ga Ma’aikatar Gona ta jiha da a je a duba wadannan gurare a kuma kawo agajin gaggawa domin magance wannan tsutsa da kuma illar da ta keyi a gonakin.

Shugaban Majalisar Rt Hon Engineer Hamisu Ibrahim Chidari bayan sauraren wannan kuduri na gaggawa da kuma tattaunashi da  aka yi a Zauren Majalisar ya yi amfani da wannan dama inda gida ya amince da ayi kiran gaggawa ga Ma’aikatar Gona da Albarkatun Kasa ta jiha da a hanzarta kawo karshen wannan tsutsa da ta ke barazanar hana noma a wadannan yankuna.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending