Connect with us

Labarai

Rahoto: Matashi ya gurfana a kotu da zargin fashi da makami

Published

on

Babbar kotun jiha mai lamba 7, karkashin mai shari’a Usman Na’abba, ta sake gurfanar da wani matashi mazaunin unguwar Badawa da zargin laifin fashi da makami da kisan kai.

Kunshin zargin ya bayyana cewar, matashin ya harbe wani mutum mai suna Sani Gwammaja da bindiga har ya hallaka shi, ya kuma dauke masa mota.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il na da cikakken rahoton.

Audio Player

Baba Suda

‘Yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki – Minista

Published

on

Ministan Wutar Lantarki, Adedayo Adelabu ya bayyana cewa kimanin ’yan Najeriya miliyan 150 ne yanzu ke samun isasshiyar wutar lantarki, yayin da miliyan 80 ke da ƙarancin wutar lantarki.

 

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a yayin taron sabunta sassan ministoci na 2025 da aka gudanar a Abuja, inda ya yi magana tare da ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris Malagi, da sauran masu ruwa da tsaki.

 

Adelabu ya bayyana cewa ci gaban ya samo asali ne daga shigar Najeriya cikin shirin “Mission 300” – wani gagarumin ƙoƙarin haɗin gwiwa na Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka (AfDB) da nufin samar da wutar lantarki ga ‘yan Afirka miliyan 300 nan da shekarar 2030.

 

Ƙa’idar ta tsara kyawawan manufofi don haɓaka hanyoyin samar da wutar lantarki, ƙara haɓaka makamashi da inganta hanyoyin magance matsalolin dafa abinci mai tsafta ga miliyoyin ‘yan Najeriya – wato Mission 300, kuma muna samun ci gaba mai kyau a kan wannan,” in ji shi.

 

Ya ci gaba da cewa, “Ina mai farin cikin gaya muku cewa cikin ‘yan Afirka miliyan 300 da Bankin Duniya da AfDB ke son cimmawa, Najeriya na kan hanyar da za ta biya ƙasa da kashi 25 cikin 100, wanda ke nufin kusan ‘yan Najeriya miliyan 75. Da muka gabatar da yarjejeniyarmu, sun amince da mu.”

Continue Reading

Daurin Boye

Mun kafa kwamiti domin rage farashin – Gwamnatin tarayya

Published

on

Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti da zaiyi Duba kan hanyoyin shigo da abinci domin rage farashin sa da kaso 50.

Kwamitin dai dake karkashin mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima zai yi aiki ne da wasu ministoci, domin ganin an wadatar Nigeria da abinci.

 

Yayin jawabin sa, Sanata Kashim Shettima yace hakan wani bangare NE na kara inganta tattalin arziki da shugaban kasa Asuwaju Bola Tinubu ke kokari.

 

Continue Reading

Labarai

Arsenal ba kanwar lasa ba ce – Me tsaron Gidan Real Madrid

Published

on

Me tsaron Gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Thibaut Courtois yace sun yi rashin nasara ne a wasan da suka buga a jiya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, saboda Arsenal din ba kanwar lasa ba ce.

A jiya Laraba ne dai aka fafata wasan kusa da na kusa da na karshe, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Arsenal Inda Arsenal ta lallasa Real Madrid da ci 2 da 1.

Continue Reading

Trending