Connect with us

Lafiya

Ana zargin namiji da afkawa wani yaro

Published

on

Babbar kotun shari’ar Musulunci dake zamanta a Kafin Mai Yaƙi a ƙaramar hukumar Kiru, ƙarƙashin mai Shari’a Ustaz Sani Salihu, ta ci gaba da sauraron shari’ar wani magidanci mazaunin garin Yako mai kimanin sama da shekaru Hamsin, da ake zarginsa da haikewa wani ƙaramin yaro ɗan kimanin shekaru Takwas.

A zaman  na ranar Litinin, ko da Ɗan Sanda mai gabatar da ƙara Sajan Aminu Ƙofar Wambai, wanda ya fito daga sashin binciken manyan laifuka dake unguwar Bompai, ya roƙi kotun, da ta bayar da izini a mayar da magidancin sashin binciken manyan laifuka, domin faɗaɗa bincike, dogaro da sashi na 298, wato Further Investigation, a nan ne Alƙalin kotun Shehun Malami Sani Salihu ya ce, Kotun za ta yi nazari kan roƙon da Sajan Aminu Ƙofar Wanbam ya yi.

Kotun ta bayar da umarnin ci gaba da tsare magidancin a gidan ajiya da gyaran hali, zuwa lokacin da ta yi nazari kan roƙon.

Bayan da aka fito daga kotun ne kuma, mu ka ji ta bakin mahaifin yaron wanda ya nemi kotun da ta nema musu haƙƙin ɗansu, domin kuwa har sau biyar yana amfani da yaron namu.

Shima kuma magidancin da ake zargi da nuna halin ta idon, ya ce, “Zargin da ake mini ba gaskiya ba ne ba, ko Alƙur’ani aka bani zan iya rantsewa akan zargin da ake mini, koda kuwa zan mutum bayan na rantse, domin ban ma san yaron da aka alaƙantani dashi ba” Inji Auwalu Coach.

 

Lafiya

Ku rinƙa ziyartar Asibiti ana muku gwaje-gwajen fitsari da Jini domin sanin halin da ƙodar ku take ciki – Likita

Published

on

An shawarci al’umma da su rinƙa ziyartar Asibiti akai akai wajen duba lafiyar su, ta hanyar yin gwaje-gwajen fitsari da jini domin sanin halin da kodar su ke ciki.

Dakta Muhajid Sunusi Rabi’u ne ya bayyyana hakan yayin ganawarsa da Dala FM, lokacin da suke aikin gwaje-gwajen fitsari da jini, kyauta a ɗaya daga cikin makarantu masu zaman kan su a nan Kano.

Dakta Mujaheed ya kuma ce sun gudanar da aikin ne a wani ɓangare na bikin ranar ƙoda ta Duniya, wadda aka ware duk ranar Alhamis ta mako na biyu na kowanne watan Maris domin gudanar da bikin ranar.

Continue Reading

Lafiya

Za’a yiwa kusan yara miliyan 3 rigakafin cutar shan Inna a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano tace kusan Yara miliyan 3 za’ayiwa rigakafin cutar shan inna a kananan hukumomin jihar nan 44, duba da samun ɓurɓushinta da kaso 65, a jihar ta Kano.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da rigakafin cutar shan innar a yau Alhamis, wanda za’a kwashe kwanaki 4 ana gudanarwa a Kano.

Dakta Abubakar Labaran ya ce duba da shigowar zafin akwai buƙatar al’umma su kula da alamomin cutar sankarau, duk da gwamnati ta yi shirin bayar da agajin gaggawa, kamar yadda tashar Dala FM Kano ta rawaito.

Ma’aikatar lafiyar ta jihar Kano dai ta ce za’a ci gaba da gudanar da sauran rigafin, domin bai wa yaran jihar Kano kariya daga cututtuka masu yaɗuwa.

Continue Reading

Lafiya

Dokar tilasta gwajin lafiya kafin aure ta tsallake karatu na biyu a majalisar dokokin Kano

Published

on

Rahotanni na bayyana cewar majalisar dokokin jihar Kano, ta yi karatu na biyu a kan kudirin dokar tilasta wa masu niyyar yin aure yin gwajin cutar kanjamau, da na cutar hanta da kuma duba kwayoyin jini wato Sikila, gabanin daura aure.

Ɗan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Takai, Hon.Musa Ali Kachako, shin wanda ya kawo kudirin dokar, ya bayyana cewa, jihar Kano na fama da matsalolin lafiya daban-daban da suka hada da cutar kanjamau saboda mutane kan yi aure ba tare da an duba lafiyarsu ba, hakan ne ma ya sa ya kai ƙudirin.

Kachako, ya ce, ƙudirin dokar idan har aka amince da shi, zai ceci rayuka da dama tare da dakile yaɗuwar cututtuka masu barazana ga rayuwar al’umma, kamar yadda jaridar Kadaura24 ta rawaito.

Da yake nuna goyon bayansa kan ƙudirin Ɗan majalisa Hon. Aminu Sa’ad, mamba mai wakiltar mazabar Ungogo, ya ce, jihohin Jigawa, Katsina da Kaduna sun zartar da irin wannan kudiri domin magance kalubalen kiwon lafiya da suke fuskanta.

Ya ce tilas ne Kano da ke da yawan al’umma a kasar nan ta zartar da kudirin dokar, domin kare lafiyar ‘yan jiharta ta hanyar samar da gwaje-gwaje kafin aure domin dakile yaduwar cututtuka, kamar cutar hanta, da sauran cututtuka.

Continue Reading

Trending