Connect with us

Labarai

Kotu: Idan Aminu Attakawa ya tsere masu karbar beli za su biya Naira Miliyan 1

Published

on

Kotun majistret mai lamba 23 karkashin mai Shari’a, Sanusi Usman Atana ta tsayar da ranar 5 ga watan gobe, domin ci gaba da shari’ar da ‘Yansanda suka gurfanar da wani mutum mai, suna Aminu Ahmad Attakawa, wanda a ke zargin sa da laifin yunkurin tayar da hankalin al umma ta kafar yada labarai.

Kunshin tuhumar ya bayyana cewar a ranar 2 ga wata ne, Aminu Attakawa, ya je gidan wani rediyo ya bayyana cewar filayen da su ke unguwar Rimin Zakara mallakar Jami’ar Bayaro ne.

Kunshin zargin ya bayyana cewar wanda a ke tuhuma ya bayyana cewar ya na da shaidu na takardu da su ka nuna cewar filayen mallakar Jami’ar ne.

Hakan ne ya sanya wa su mazauna Rimin Zakara su ke da’awar filayen mallakin su ne su ka shigar da kara a kan wannan ikirari.

A zaman kotun na yau an karanta kunshin tuhumar, kuma magatakardar kotun, Inusa Sule Beli, shi ne ya fassara kunshin zargin sai dai Aminu Attakawa ya musanta. Kotun ta sanya shi a hannun beli bisa sharadin sai ya kawo mutum 2 daya fitaccen dan kasuwa dayan kuma mai matakin albashi na 15, an kuma umarce shi kar ya sake yin maganar ta kowace kafa har zuwa karshen Shari’ar. wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail, ya rawaito cewar kotun ta bayyana cewar idan, Aminun ya tsere masu karbar belin za su biya Naira miliyan daya.

Ilimi

Mun shirya yin aiki tare da masarautar Gaya – SEDSAC

Published

on

Kungiyar bunkasa ilimi da ci gaban demokradiya ta SEDSAC ta ce masarautar Gaya itace masarauta ta farko da kungiyar za ta yi hadin gwiwa da ita, domin ci gaba da samar da shirye-shirye da ya shafi rayuwar al’umma.

Sanarwar ta fito ne ta hannun daraktan kungiyar, Kwamrade Umar Hamisu Kofar Na’isa, ta na mai cewa, za ta yi hadin gwiwa da dukannin masauratu Biyar na Kano, domin bunkasa rayuwar al’umma tare da samar da ci gaba a kasa.

SEDSAC ta kuma yabawa gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje da kuma ma su zaben sarki a Gaya, bisa nada Alhaji Ali Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin sabon sarkin Gaya, wanda kuma ya na daya daga cikin jigon iyaye na kungiyar SEDSAC.

Haka zalika SEDSAC ta kuma taya sabon sarkin murnar sarautar da ya samu tare da yi wa marigayi tsohon Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir Gaya, addu’ar neman gafara a wajen Ubangiji.

Continue Reading

Labarai

Ba ma samun kulawa a wajen Gwamnati – Masu sana’ar Shuke-shuke

Published

on

Kungiyar masu Shuke-shuke ta kasa reshen jihar Kano ta koka dangane da rashin kulawa daga gwamnati wajen siyan tsirrai daga wurin su.

Shugaban kungiyar, Aliyu Shehu Kabara, ya bayyana hakan, yayin taron shekara da suka gudanar a jihar Kano a karshen makon da ya gabata.

Ya na mai cewar, “Yawancin lokuta gwamnati kan tashi masu sana’ar Shuke-shuke ba tare da samar musu da wasu wuraren ba”. Inji Aliyu Shehu Kabara.

A nasa jawabin, wani masani a kan harkokin tsirrai daga Jami’ar Bayero ta Kano, Malam Hassan Usaini, ya ce, “Akwai gudunmawa mai tarin yawa da masu lambuna ke bayarwa, a fannin muhalli da kuma ilimi, wanda suma mata akwai bukatar su shigo cikin harkar domin bayar da gudunmawa”.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya ruwaito cewar, masu lambunan sun yi fatan gwamnati da sauran hukumomi, za su hada hannu da su, domin samar da ingantaccen muhalli.

Continue Reading

Labarai

Za mu hana shan Shisha a bainar Jama’a – Hukumar yawon bude ido

Published

on

Hukumar yawon bude ido ta jihar Kano ta ce, za ta hana shan Shisha a bainar Jama’a tare da hana kananan yara zuwa Otel da zarar gwamnati ta sanya wa dokar hannu.

Babban Manajan Daraktan hukumar, Yusuf Ibrahim Lajawa ne ya bayyana hakan,  a ganawar sa da gidan radiyon Dala a ranar Litinin.

Ya ce, “Tsofaffin wuraren da ake gudanar da Rini, dama wuraren da ake gudanar da Jima, na daya daga cikin ababen da mu ka sanya, a cikin  kasafin kudin hukumar a Bana”. A cewar Lajawa.

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewa, Yusuf Ibrahim Lajawa ya kuma ce, aikin hukumar ta su ya ta’allaka ne kadai wajen janyo ra’ayoyin al’umma, daga ko’ina domin zuwa jihar Kano domin yawon bude ido.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!