Connect with us

Labarai

Kano: An samu hatsaniya tsakanin direbobin Tirela da KAROTA da Road Safety

Published

on

Safiyar Lahadi ne a ka samu wata hatsaniya tsakanin Direbobin Tirela da jami’an hukumar kiyaye afkuwar haɗura da na hukumar Karota a Sabon Titin Panshekara dake yankin ƙaramar hukumar Gwale, inda su ka rufe hanyar babu wucewa baki ɗaya a lokacin.

A zantawar wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u da wani Direban Tirelan mai suna, Tasi’u Musa Yusuf, tare da wani Direba a wajen sun ce, sun rufe hanyar ne bisa zargin farfasa musu gilashi da cire lamba, da kuma cirewa wani Direba batir ɗin motarsa da jami’an hukumomin biyu su ka yi, inda Direbobin su ka ce ba za su buɗe hanyar ba, har sai an biya su ɓarnar da a ka yi musu.

A kan hakan ne wakilin namu ya tuntuɓi mai magana da yawun hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta Road Safety ta jihar Kano, sai dai ya ce a jirawo za su bincika, haka shi ma mai magana da yawun hukumar Karota, Nabulisi Abubakar Ƙofar Na’isa ya ce zai bincika.

Kasancewar jami’an ‘ƴan sanda sun halarci wajen da al’amarin ya faru tare da kama wa su matasa da a ke zargi da farfasa gilashin motar jami’an hukumar kiyaye afkuwar haɗurar, hakan ne ya sa wakilin namu ya tuntuɓi Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ta wayar tarho, sai dai har zuwa yanzu bamu same shi ba.

Motar da a ka fasa gilashin ta.

Direbobin dai sun rufe hanyar ne ta Panshekara daga ƙarfe 7 har zuwa karfe kusan 10:45 na safe, kamar yadda wakilin namu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito mana.

Labarai

Aure: Haramin ne mace ta fita daga gida ba tare da izini ba – Dr Abdallah

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Usman Bin Affan dake unguwar Gadan Ƙaya, Dakta Abdullah Usman Umar ya ce, ba dai-dai ba ne mata su rinƙa fita duk inda su ka so zuwa, ba tare da neman iznin mazajen su ba.

Dakta Abdallah Gadon Ƙaya ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Rayuwa Abar Koyi na nan gidan rediyon Dala FM, wanda ya gudana da safiyar Juma’a.

Ya ce”Fitar da wasu matan ke yi ba tare da neman izinin mazajen su ba yin hakan saɓawa ne, kuma bai kamata mata su rinƙa cin mutuncin mazajen su ba, domin kuwa raina miji raina addini ne”. A cewar Dakta Aballah.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Dakta Abdullah Gadan Ƙaya, ya kuma shawarci magidan ta, da su kaucewa yin azalo ga matan su, domin yin hakan ba dai dai ba ne ba a tsarin addinin Musulunci.

Continue Reading

Labarai

Shan Kwayoyi: Kowa sai ya bayar da gudunmawa a bangaren- Farfesa Hafsat Ganduje

Published

on

Matar gwamnan Kano, Farfesa Hafsat Umar Ganduje, ta ce yaki da shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasa ba zai tabbata ba, har sai kowa ya bayar da gudunmawar sa a fannin.

Farfesa Hafsat Ganduje ta bayyana hakan ne, a yayin wani rabon bayar da tallafin kekuna da kayan karatu ga dalibai, wanda ya gudana a  hukumar Shari’a.

Ta ce”Gwamnatin Kano na iya kokarin ta wajen yaki da shan miyagun kwayoyi, amma duk da haka sai kowa ya shigo ya bayar da ta sa gudunmawar, yanzu haka gwamnatin Kano ta kara daura dammara wajen gyara tare da samar da kayayyakin da a ke da bukata a makarantar gyaran hali dake karamar hukumar Kiru”. Inji Farfesa Hafsat Ganduje.

Wakilin mu Ahmad Rabi’u Ja’en ya rawaito cewa, a yayin bayar da tallafin an raba kekunan hawa da jakunkuna na makaranta ga wasu daga cikin daliban Firamare.

Continue Reading

Labarai

Rahoto:  Mu kara godiya ga Allah da mu ka sake ganin watan Mauludi – Limamin Gwazaye

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Ammar bin Yasir da ke unguwar Gwazaye gangar ruwa a karamar hukumar Gwale, Malam Zubairu Almuhammdi ya ce, musulmi su kara jaddada godiyar su kasancewar su na cikin al’ummar manzon Allah (S.A.W).

Malam Zubairu Almuhammdi, ya bayyana hakan ne yayin da ya ke yi wa gidan rediyon Dala FM karin bayanin abin da hudubarsa ta kunsa.

Domin jin cikakken bayanin hudubar saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!