Labarai
Sauke Ibrahim Khalil: Kwadayi ya janyo wasu malamai yin tawaye – Abdullahi Danfodio

Masanin magungunan addinin musulunci a jihar Kano, malam Abdullahi Idris Danfodio ya ce, abin takaici ne a samu malamai su na yiwa shugaba tawaye, domin yin hakan haramun.
Malam Abdullahi Danfodio, ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu na ‘yan Zazu Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.
Ya na mai cewa, “Saboda me malamai za su yiwa shugaba tawaye, bayan sun san hakan ya kaucewa koyarwar addinin musulunci”
Ya kuma ce, “Abin takaici dukkan malaman ba za a gan su a masallaci daya su na sallah ba, amma sai ga shi wata bukata ta yin tawaye ga shugaba ta hada su waje guda”. Inji Malam Abdullahi Danfodio
A jiya ne dai wasu ɓangarori daban-daban na kungiyoyin addinin musulunci su ka fitar sanarwar tsige shugaban majalisar malamai ta jihar Kano, malam Ibrahim Khalil , aka maye gurbin sa da Farfesa Abdallah Sale Pakistan.
Labarai
Rahoto: Dalibi ya kawo credit 9 a qualifying ya yi tsauri da yawa – Mai duba jarabawa

Wani tsohon mai duba sakamakon jarabawar qualifying a jihar Kano ya ce, ana duba gazawar biyawa dalibai kudin jarabawar qualifying ne yayin fitar da sakamako, saboda haka akwai rashin adalci akan lallai sai dalibai sun kawo credit 9
Tsohon mai duba sakamakon jarabawar, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.
Muna da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.
Labarai
Rahoto: Yadda hadarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2 a Lambu

Wasu motoci babba da karama, sun yi taho mu gama akan titin garin Lambu da ke karamar hukumar Tofa a jihar Kano, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane biyu, daya kuma ya jikkata.
Wasu da al’amarin ya faru a gaban idanunsu, sun bayyanawa wakilin mu na ‘yan Zazu , Abubakar Sabo cewar, mai karamar motar ne ya yi a ran hannu, wanda ya janyo faruwar hadarin.
Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.
Labarai
Babban Labari: Mun kama mota makare da kayan fashewa da bindugu da harsashi a Kano – Kiyawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sami nasarar cafke wata mota makare da wasu kayayyakin da ake hada abubuwan fashewa da kuma bindigu kirar AK47 .
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya ce, sun samu nasarar kama motar kirar Mercedez a unguwar Bubbugaje dake karamar hukumar Kumbotso.
A cewar Kiyawa sun sami rahoran sirri ne akan motar wadda suke zargin an kawo ta daga Jihar Jigawa zuwa Kano makare da irin kayayyakin da suke zargin da sune ake hada abubuwan fashewa domin aikata ta’addanci.
Sanarwar ta kuma ce bayan samun rahotan sirri na kara sowar motar zuwa Kano, jami’an tsaron Puff Adder suka yi wa mator kawanya, wanda hakan yasa mutanan ciki suka tsere suka bar motar a nan.
“Mun samu nasarar gano bindiga kirar AK47 guda biyu da kuma kananan bindigu biyu kirar Pistol tare da alburusai dubu daya da dari takwas”. In ji Kiyawa.
-
Nishadi2 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai2 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai2 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai2 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Manyan Labarai2 years ago
Ba’amurkiya da masoyin ta sun hada cinkoso a kasuwar Sabon Gari