Connect with us

Labarai

Siyasa: Al’umma su zabi nagartaccen mutum a zabe – Farfesa Kamilu Fagge

Published

on

Masanin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayaro da ke jihar Kano, Farfesa Kamilu Saminu Fagge, ya ce yawaitar samun zaben da bai kammala ba wato (Inconculusive) lokacin zabe abu ne da ka iya gurgunta demokradiyya a cikin kundin tsarin mulkin kasar nan.

Farfesa Kamilu ya bayyana hakan ne a ganawarsa da Dala ya na mai cewar,”Wa su daga cikin ma su madafin iko, na amfani da Inconculusive wajen cimma muradansu, ya kamata al’umma su lura da wanda za su zaba idan lokacin zabe ya yi”.

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewa, Farfesa Kamilu Saminu Fagge ya Ja hankalin al’umma da su zabi nagartaccen mutum, ko da bai taba tsayawa takara ba.

Labarai

Rahoto: Mu tuba ga Allah domin fita daga tsanani – Limamin Na’ibawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Nana Aisha da ke unguwar Na’ibawa Gabas, Malam Abubakar Jibril ya ce, al’umma su tuba zuwa ga Allah, domin ya musanya tsanani zuwa yanayi na walwala.

Malam Abubakar Jibril, ya bayyana hakan ne ta cikin Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke ƙasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rashin wadatar zuci ke janyo zalinta a tsakanin al’umma – Limamin CBN Quarters

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Faruq Unguwa Uku CBN Quarters, Dr. Aminu Ismai’l, ya ce, rashin wadatar zuci ke janyo zalunci da cutar wa a tsakanin al’umma.

Dr. Aminu Isma’il, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ke yi wa Dala FM ƙarin bayani dangane da Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu guji yin ƙarya da yaɗa ta – Limamin Chiranchi

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Sheikh Aliyu Harazimi da ke unguwar Chiranchi, a ƙaramar Hukumar Kumbotso, Dr Rabi’u Tijjani Rabi’u, ya ja hankalin al’ummar Musulmi da su guji yin ƙarya da kuma yaɗa ta.

Dr. Rabi’u ya bayyana hakan ne, yayin da yake ƙarin haske dangane da abin da huɗubar sa ta ƙunsa.

Wakilin mu na ƴan Zazu, Abba Isah Muhammad na da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!