Connect with us

Labarai

Banbancin aƙida: Ban yarda da shaidar da aka bayar ba – Abduljabbar

Published

on

Babbar kotun shari’ar Musulunci mai zamanta a ƙofar Kudu, ƙarƙashin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, ta ci gaba da sauraron shaida a ƙunshin zargin da gwamnatin Kano ta ke yi wa Abduljabbar Nasiru Kabara.

A zaman kotun na ranar Alhamis, Abduljabbar Kabara ya yi suka a kan shaida na biyu, wanda masu gabatar da ƙara su ka kawo.

Wanda ake tuhumar ya bayyana wa kotun cewar, shi mai bayar da shaidar su na da banbancin aƙida, domin shekaru 6 kenan, ya rubuta littafi ya ci mutuncin sa, ya kuma nuna wa kotun littafin, sai kuma wasu hotuna da Abduljabbar ya nuna da wasu rubuce-rubace, wanda shaida ya yi a shafinsa na Facebook, da ya ke nuni da cewar tsakanin shaida da wanda ake tuhumar akwai husuma.

Lauyan gwamnati Barrister Surajo Sa Ida ya roƙi kotun da ta karɓi shaidar, domin doka ta yarda koda akwai husuma tsakanin wanda ake tuhuma da Shaida za a iya yarda da shaidar.

Sai dai lauyan Abduljabbar Barrister Muhammad Aminu Mika’il ya yi suka inda ya bayyana cewar, ba a karɓar shaidar abokin husuma.

Wakilin mu Yusuf Nadabo ya rawaito cewar, kotun ta ce za ta bayyana ra’ayinta a kan batun karɓar shaidar ko watsi da ita nan gaba, kotun ta ɗage zaman shari’ar zuwa ranar 9 g watan gobe.

Labarai

Rahoto: Dokar hana shan shisha ta fara aiki gadan-gadan a Kano – Hisba

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simamen shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama dillalan Shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita.

A zantawar daya daga cikin masu shagunan sayar da Shisha da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, ya bayyana cewar, ya yi tunanin dokar hana shan Shisha ta tsaya kan masu wuraren shan Shisha ba masu sayarwa ba.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Shekaru 10 ina sarrafa Turoso amma ko ciwon kai ban taba yi ba – Mai Turoso

Published

on

Wani magidanci mai sana’ar sarrafa Turoso a yankin Kududdufawa ya ce, sama da shekaru goma ya na aikin sarrafa Turoso, amma ko ciwon kai bai taba yi ba.

Malam Isah Musa Katsinawa mazunin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Gobara ta lakume ran mutane 3 ciki harda dattijuwa

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ta kai tallafi wani gida da aka samu iftila’in gobara, wanda ta yi sanadiyar rasa mutane Uku  a unguwar Gama A, da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin mu na ‘yan zazu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, hukumar karkashin shugabanta Salihu Aliyu Jili, ta kuma kai tallafi gidan iyayen Hanifa, dalibar da aka yi zargin malaminta ya kashe ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending