Connect with us

Labarai

Za mu rufe tsohon ofishin jam’iyar APC a Kano – Sha’aban Sharada

Published

on

Babbar kotun birnin tarayya Abuja, ta sauke zaben shugabannin jam’iyyar APC a jihar Kano na bangaren gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Mai shari’a Hamza Mu’azu ne ya tabbatar da saukezaben a ranar Talata, wanda ya amince da zaben da bangaren, Sanata Ibrahim Shekarau kuma Ahmad Haruna Zago shi ne a matsayin halastaccen shugaban jam’iya.

Alkalin ya yanke hukuncin ne cewa, tsagin tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata mai ci a yaznu, Malam Ibrahim Shekarau su ne shugaban jam’iyar a yanzu.

A cewar mai shari’ar zaben na bangaren Shekarau ya samu sanya hannun mutum 7 daga cikin wadanda uwar jam’iyyar ta turo jihar Kano, domin gudanar da zaben.

Cikin abin da tsagin Shekarau ya gabatar, gaban kotun shi ne tsagin na gwamna Ganduje bai gudanar da zaben matakin kanan nan hukumomi da mazabu ba.

Idan za a iya tunawa a watan da ya gabata ne aka gudanar da zaben shugabancin jam’iyya APC a jihohin kasar nan ciki har da nan Kano, wanda a ka samu sa’insa a tsakanin ‘yan siyasa a jam’iyar ta APC a Kano.

Sai dai a wata tattaunawa da suka yi da Nasiru Salisu Zango ta wayar tarho, sakataren jam’iyar APC a Kano tsagin gwamnan Kano, Ahmed Aruwa, Ɓangaren Abdullahi Abbas, ya ce“za mun daukaka kara zuwa kotun daukaka kara, kuma wannan ba wani labara ba ne da zai dagawa mutane hankali ba”.

Shi kuwa Sha’aban Ibrahim Sharada tsagin Malam Ibrahim Shekarau, cewa ya yi”Mu dai sai dai mu godewa Allah bisa wannan nasarar da kotu ta yanke hukunci, kuma za mu bude sabon ofishi a dukannin mazabu, daga baya kuma sai a bude a kananan hukumomi 44, bayan an bude na jiha, kuma za mu rufe tsohon ofishin Abdullahi Abbas, saboda ba shi ne shugaba ba a yanzu”.

Hangen Dala

Zargin Almundahana:- An kama jami’in gwamnatin Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama Tasiu Al’amin-Roba, babban mataimaki na musamman (SSA), ga gwamnan jihar kano da kuma wani Abdulkadir Muhammad bisa zargin su da karkatar da kayan abincin tallafi a jihar Kano.

 

Kwamishinan ‘yan sandan, Hussaini Gumel, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN hakan a wata hira ta wayar tarho a ranar Lahadi cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wani dakin ajiyar kaya da ke Sharada dauke da jakunkuna sama da 200.

 

Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun yi awon gaba da shinkafa da masara a ma’ajiyar da ke Sharada.

 

“Tun daga lokacin ne muka fara bincike mai zurfi don gano buhunan masara ko shinkafa nawa aka diba aka sayar da su,” inji shi.

 

Gumel ya ce za a gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu bayan kammala bincike .

Continue Reading

Hangen Dala

An yiwa kasafin Kudin 2024 karatu na biyu

Published

on

Majalisar Dattawan Najeriya da ta Wakilai sun yi wa kasafin kuɗin ƙasar na 2024 karatu na biyu ranar Juma’a kwana biyu bayan Shugaba Bola Tinubu ya gabatar musu da shi.

A ranar Laraba ne Tinubu ya je majalisar tare da gabatar da naira tiriliyan 27.5 a matsayin kasafin abin da gwamnatinsa za ta kashe a 2024, kuma ya nemi ‘yan majalisar su gaggauta amincewa da shi.

Sai dai shugaban bai bayyana adadin abin da kowace ma’aikata da hukumomin gwamnati za su samu ba a lokacin da ya yi gabatarwar, abin da ya jawo cecekuce da muhawara a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito ‘yan majalisar na kokawa yayin muhawarar da suka yi ranar Juma’a game da ƙarancin bayanai kan kasafin, wanda suka ce ya sa sun mayar da hankali ne kawai kan abubuwan da Tinubu ya faɗa a jawabinsa.

Jam’iyyun adawa sun soki kasafin da cewa “na yaudara ne”, yayin da Shugaba Tinubu ya yi masa laƙabi da “kasafin sabunta fata”.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin Kano za ta Kara inganta aikin Jarida

Published

on

Gwamnatin jihar kano tace za ta hada Kai da kungiyar ‘yan jarida masu magana a Radio da Television na kasa wato Society of Nigerian Broadcasters domin kara inganta aikin Jarida.

 

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Baba Halilu Dan Tiye ne ya tabbatar da hakan lokacin da ake kaddamar da ‘ya’yan kungiyar anan kano.

 

Baba Halilu yace duba da muhimmancin da aikin jarida ke dashi a tsakanin al’umma ya sanya gwamnatin Kano za ta cigaba da baiwa bangaren muhimmanci.

Taron Wanda ya gudana a cibiyar ‘yan Jaridu ta Kano ya samu halartar Mafi yawa daga cikin shugabannin kafafen yada labaran Dake Kano.

Continue Reading

Trending