Connect with us

Labarai

Ba za mu laminci dawo da siyasar ta’addanci ba a Kano – PDP

Published

on

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano, ta yi tir da harin da ƴan daba suka kai ofishin Sanata Barau Jibrin a jihar.

Hakan na cikin wani saƙon murya da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar, Bashir Sanata ya aike wa Freedom Radio.
A cikin saƙon Sanata ya zargi jam’iyyar APC da yunƙurin dawo da siyasar daba a Kano.

Ya ci gaba da cewa,”Ya kamata APC ta sani an riga an wuce irin wannan siyasar. A lokacin mu mun samarwa matasa aikin yi, saboda bamu yarda da irin wannan tsarin ba, amma yanzu a na ƙoƙarin mayar da Kano baya”.

Ya ci gaba da cewa,”Ya kamata APC ta sani an riga an wuce irin wannan siyasar. A lokacin mu mun samarwa matasa aikin yi, saboda bamu yarda da irin wannan tsarin ba, amma yanzu a na ƙoƙarin mayar da Kano baya”.

Ya ƙara da cewa “Matasan nan da su mu ke alfahari, idan ka gina su ka gina al’umma, amma idan wasu ƴan siyasa na amfani da matasa, domin daba to hakan ba zai haifar mana ɗa mai ido ba”. Inji Bashir Sanata.

A wannan makon mai ƙarewa ne jam’iyyar APC tsagin tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau su ka zargi ɓangaren, Gwamna Abdullahi Ganduje da kai wa ofishin yaƙin neman zaɓen Sanata Barau Jibrin hari.

Sai dai kuma tuni tsagin Gwamna Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya musanta wannan zargi.

Labarai

Rahoto: Dalibi ya kawo credit 9 a qualifying ya yi tsauri da yawa – Mai duba jarabawa

Published

on

Wani tsohon mai duba sakamakon jarabawar qualifying a jihar Kano ya ce, ana duba gazawar biyawa dalibai kudin jarabawar qualifying ne yayin fitar da sakamako, saboda haka akwai rashin adalci akan lallai sai dalibai sun kawo credit 9

Tsohon mai duba sakamakon jarabawar, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.

Muna da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Yadda hadarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2 a Lambu

Published

on

Wasu motoci babba da karama, sun yi taho mu gama akan titin garin Lambu da ke karamar hukumar Tofa a jihar Kano, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane biyu, daya kuma ya jikkata.

Wasu da al’amarin ya faru a gaban idanunsu, sun bayyanawa wakilin mu na ‘yan Zazu , Abubakar Sabo cewar, mai karamar motar ne ya yi a ran hannu, wanda ya janyo faruwar hadarin.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Babban Labari: Mun kama mota makare da kayan fashewa da bindugu da harsashi a Kano – Kiyawa

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sami nasarar cafke wata mota makare da wasu kayayyakin da ake hada abubuwan fashewa da kuma bindigu kirar AK47 .

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya ce, sun samu nasarar kama motar kirar Mercedez a unguwar Bubbugaje dake karamar hukumar Kumbotso.

A cewar Kiyawa sun sami rahoran sirri ne akan motar wadda suke zargin an kawo ta daga Jihar Jigawa zuwa Kano makare da irin kayayyakin da suke zargin da sune ake hada abubuwan fashewa domin aikata ta’addanci.

Sanarwar ta kuma ce bayan samun rahotan sirri na kara sowar motar zuwa Kano, jami’an tsaron Puff Adder suka yi wa mator kawanya, wanda hakan yasa mutanan ciki suka tsere suka bar motar a nan.

“Mun samu nasarar gano bindiga kirar AK47 guda biyu da kuma kananan bindigu biyu kirar Pistol tare da alburusai dubu daya da dari takwas”. In ji Kiyawa.

Continue Reading

Trending