Connect with us

Labarai

Ba za mu sanya idanu shugabbani na yin nisa da al’umma – Kwamrade Saddat

Published

on

Shugaban Ƙungiyar haɗin kan Arewacin Najeriya, Kwamared Saddat Usman Mai Yaƙi, ya ce, kamata ya yi gwamnatin tarayya ta ƙara lalubo hanyoyin da za a tallafawa matasan ƙasar nan, domin fitar da su daga halin da suke ciki na taɓarɓarewar rayuwa.

Kwamared Sadat ya bayyana hakan ne a yayin taron haɗin kan al’ummar Arewacin ƙasar nan, wanda ƙungiyar ta gudanar a ɗakin taro na ƙungiyar da ke kan titin Maiduguri, wanda a kayi a ƙarshen makon da ya gabata.

Ya ce,”Bai kamata gwamnati ta rinƙa nuna halin ko in kula ba da matasan Arewacin ƙasar nan ba”. Inji Kwamrade Saddat.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u da ya halarci taron ya rawaito cewa, babban jami’in ƙungiyar Kwamared Shaddat ya ce, ba zasu cigaba da sanya idanu shugabanni suna yin nisa da al’umma ba musamman ma a wannan lokaci.

Labarai

Rahoto: Dalibi ya kawo credit 9 a qualifying ya yi tsauri da yawa – Mai duba jarabawa

Published

on

Wani tsohon mai duba sakamakon jarabawar qualifying a jihar Kano ya ce, ana duba gazawar biyawa dalibai kudin jarabawar qualifying ne yayin fitar da sakamako, saboda haka akwai rashin adalci akan lallai sai dalibai sun kawo credit 9

Tsohon mai duba sakamakon jarabawar, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.

Muna da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Yadda hadarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2 a Lambu

Published

on

Wasu motoci babba da karama, sun yi taho mu gama akan titin garin Lambu da ke karamar hukumar Tofa a jihar Kano, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane biyu, daya kuma ya jikkata.

Wasu da al’amarin ya faru a gaban idanunsu, sun bayyanawa wakilin mu na ‘yan Zazu , Abubakar Sabo cewar, mai karamar motar ne ya yi a ran hannu, wanda ya janyo faruwar hadarin.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Babban Labari: Mun kama mota makare da kayan fashewa da bindugu da harsashi a Kano – Kiyawa

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sami nasarar cafke wata mota makare da wasu kayayyakin da ake hada abubuwan fashewa da kuma bindigu kirar AK47 .

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya ce, sun samu nasarar kama motar kirar Mercedez a unguwar Bubbugaje dake karamar hukumar Kumbotso.

A cewar Kiyawa sun sami rahoran sirri ne akan motar wadda suke zargin an kawo ta daga Jihar Jigawa zuwa Kano makare da irin kayayyakin da suke zargin da sune ake hada abubuwan fashewa domin aikata ta’addanci.

Sanarwar ta kuma ce bayan samun rahotan sirri na kara sowar motar zuwa Kano, jami’an tsaron Puff Adder suka yi wa mator kawanya, wanda hakan yasa mutanan ciki suka tsere suka bar motar a nan.

“Mun samu nasarar gano bindiga kirar AK47 guda biyu da kuma kananan bindigu biyu kirar Pistol tare da alburusai dubu daya da dari takwas”. In ji Kiyawa.

Continue Reading

Trending