Connect with us

Addini

Rundunar Yan sandan Kano ta gargadi mutane a kan bikin Kirsimeti da sabuwar shekara

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Kano ta ce za ta bayar da cikakken tsaro, domin ganin an gudanar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara cikin kwanciyar hankali da lumana.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma’a.

Ya ce”Rundunar mu a shirye ta ke tsaf wajen haramta harba knockout tare da masu kona tayoyi, saboda haka kowa ya tabbata ya bamu gudunmawa wajen ganin komai ya tafi lafiya, iyaye su jawa ‘ya’yan su kunne”. Inji DSP Kiyawa.

Rundunar ta kuma gargadi masu yin gudun ganganci da mota da su kiyaye doka tare da ganin bas u yi wasan tseren mota ba, musamman ma a murnar sabuwar shekara ta 2022.

Addini

Rahoto: Kafin mutum ya mutu ya bar abinda za a tuna da shi na alheri – Limamin Bompai

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke Bompai, SP Abdulkadir Haruna ya ce, ana bukatar mutum ya bar abinda za a rinka yabonsa da shi bayan baya duniya.

SP Haruna, ya bayyana hakan ne, ta cikin hudubar Juma’a da ya gabatar, ya na mai cewa, su mutane shaidun mutane ne a bayan kasa.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad, na da cikakkiyar hudubar.

Continue Reading

Addini

Rahoto: Mu yi amfani da idanu wajen kallon alheri – Limamin Tukuntawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Masjidul Kuba da ke unguwar Tukuntawa, malam Ibrahim Abubakar Tofa ya ce, akwai bukatar musulmai su yi amfani idanun su wajen aikata alheri.

Malam Ibrahim Abubakar Tofa, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, dangane da abinda hudubarsa ta kunasa.

Akwai cikakkiyar hudubar a cikin muryar kasa.

 

Continue Reading

Addini

Rahoto: A guji kallon Fina-finai a watan Ramadan – Limamin Unguwa Uku

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Faruq Unguwa Uku CBN Quarters, Dr Abdulkadir a jihar Kano ya ce, a guje wa kallon fina-finani a watan Ramadan, domin samun kusanci da Ubangiji.

Dr Abdulkadir Ismai’l, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da gidan rediyon Dala, dangane da abinda  hudubar Juma’a da ya gabatar ta kunsa.

Akwai cikakken bayanin hudubar a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Trending