Connect with us

Labarai

Kano: ‘Yan bindiga sun sace mahaifiyar dan majalisa a Kano

Published

on

Wasu ‘yan bindiga sun sace mahaifiyar shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin Jihar Kano, Isiyaku Ali Danja da tsakar daren ranar Laraba.

‘Yan bingigar sun kutsa kai zuwa gidan, Hajiya Zainab da ke karamar hukumar Gezawa da misalin ƙarfe 1:00 na dare ɗauke da makamai, inda su ka tilasta wa mutan gidan cewa sai an kai su ɗakinta.

Saminu Danja wanda ɗa ne ga ɗan majalisar, ya faɗa wa BBC cewa ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ɓarayin ba su tuntuɓe su ba.

Honorabul Isiyaku Ali Ɗanja, shi ne tsohon Kakakin Majalisar Kano kuma wakilin Gezawa a majalisar.

Yankin Arewa maso Yammacin Najeriya na ci gaba da fuskantar sace-sacen mutane, domin neman kuɗin fansa, sai dai lamarin bai yi ƙamari a Kano ba kamar jihohi maƙotanta.

Labarai

Rahoto: Dokar hana shan shisha ta fara aiki gadan-gadan a Kano – Hisba

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simamen shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama dillalan Shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita.

A zantawar daya daga cikin masu shagunan sayar da Shisha da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, ya bayyana cewar, ya yi tunanin dokar hana shan Shisha ta tsaya kan masu wuraren shan Shisha ba masu sayarwa ba.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Shekaru 10 ina sarrafa Turoso amma ko ciwon kai ban taba yi ba – Mai Turoso

Published

on

Wani magidanci mai sana’ar sarrafa Turoso a yankin Kududdufawa ya ce, sama da shekaru goma ya na aikin sarrafa Turoso, amma ko ciwon kai bai taba yi ba.

Malam Isah Musa Katsinawa mazunin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Gobara ta lakume ran mutane 3 ciki harda dattijuwa

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ta kai tallafi wani gida da aka samu iftila’in gobara, wanda ta yi sanadiyar rasa mutane Uku  a unguwar Gama A, da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin mu na ‘yan zazu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, hukumar karkashin shugabanta Salihu Aliyu Jili, ta kuma kai tallafi gidan iyayen Hanifa, dalibar da aka yi zargin malaminta ya kashe ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending